Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 a Borno (Hotuna)

Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 a Borno (Hotuna)

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Borno tayi bajakolin masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 da ta kama tare da kayan laifi da makaman su a hedikwatar rundnar dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Masu laifin da aka yi bajakolin sun hada da 'yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane, wadanda suka aikata laifin kisa da kuma dillalan miyagun kwayoyi da sauran kayan maye.

Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 a Borno (Hotuna)
Rundunar 'yan sanda tayi masu laifi da 'yan ta'adda a Borno

Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 a Borno (Hotuna)
Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda a Maiduguri

Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 a Borno (Hotuna)
Kayan laifi
Asali: Twitter

Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 a Borno (Hotuna)
Masu laifi da 'yan ta'adda
Asali: Twitter

Daga jihar Adamawa mai makwabataka da jihar Borno, kun ji cewar kwamishinan 'yan sanda a jihar, Adamu Audu Madaki, ya tabbatar da cewar rundunar 'yan sanda ta tsare wata ungulu da jama'a suka shigar da korafin cewar basu yarda da ita ba.

Kwamishinan ya bayyana cewar an tsare ungulun ne biyo bayan korafin da jama'a suka shigar.

Madaki ya ce a ranar Litinin ne wasu jama'a daga yankin karamar hukumar Maiha suka shigar da korafi a ofishin 'yan sanda a kan wata ungulu mallakar wata mata dake yankin su.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Borno ta mayar da gidan yari makarantar firamare (Hotuna)

Mazauna yankin sun ce ganin Ungulun na tayar musu da hankali, a saboda haka basu yarda da ita ba.

Sun yi zargin cewa a lokaci na karshe da suka ga wasu Ungulu uku a yankin su, harin mayakan kungiyar Boko Haram ne ya biyo baya.

A cewar jaridar Sun, al'ummar yankin sun bukaci 'yan sanda su tilasta wa matar da Ungulun ta barin yankin da suke. Bayan gudanar da bincike, rundunar 'yan sanda ta kama matar da Ungulun ta kuma yanzu haka an mayar da su hedikwatar 'yan sanda dake Yola domin zurfafa bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel