'Yan sanda sun kama mutumin da ya yiwa abokanan sa ihun kidinafas a Kaduna

'Yan sanda sun kama mutumin da ya yiwa abokanan sa ihun kidinafas a Kaduna

- 'Yan sanda sunyi nasarar kama wannan takadirin mutumin da ya yiwa abokanan sa ihun masu garkuwada mutane a tashar Kawo dake Kaduna, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku

- Mutumin wanda abokanan nasa suka zo daga Lagos domin tafiya dashi, bayan sun tsaya masa a matsayin shaidu a kotu ya samu belin fitowa, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane ukun

A jiya Talata ne jami'an hukumar 'yan sanda suka yi nasarar cafke Alhaji Musa Imam, mutumin da ya yi ihun karya akan masu garkuwa da mutane za su sace a tashar Kawo dake Kaduna, inda hakan ya yi sanadiyyar mutane uku.

Abokanan Imam sun biyo shi ne tun daga Lagos, bayan sun tsaya mishi a matsayin shaidu a kotu ya samu beli shine ya gudo Kaduna, bayan zuwan su gadar Kawo sai ya yi ihun cewa mutanen suna so su sace shi ne.

Ihun na shi ne ya yi sanadiyyar jawo hankalin al'ummar da ke yankin, inda suka sanyawa motar da suke ciki wuta biyu daga cikinsu suka samu nasarar shiga gidan man dake kusa inda suka samu 'yan sanda suka kwace su da kyar.

'Yan sanda sun kama mutumin da ya yiwa abokanan sa ihun kidinafas a Kaduna

'Yan sanda sun kama mutumin da ya yiwa abokanan sa ihun kidinafas a Kaduna
Source: UGC

A kokarin da jami'an tsaron suke na ganin sun fita da mutanen daga gurin, sai da hakan ya yi sanadiyyar suka harbi mutane uku.

Bayan ya jawo hankalin mutanen da suka yi sanadiyyar kashe direban motar, Alhaji Musa Imam ya samu ya gudu.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo, a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa sun samu nasarar cafke Alhaji Musa Imam da misalin karfe 5 na yamma jiya Talata.

KU KARANTA: An yanka ta tashi: Mutanen da aka kashe aka kone a Kaduna 'yan sanda ne ba masu satar mutane ba

Sanarwar ta bayyana cewa mutum daya da jami'an tsaron suka harba a lokacin da suke kokarin ceto ran sauran mutane biyun ya mutu, inda hakan ya sanya yawan mutanen da suka mutu suka zama uku duka sanadiyyar karyar da Alhaji Musa Imam ya yi.

Jami'in dan sandan ya ce 'yan sandan jihar Legas sun kira mutane ukun da suka tsaya a matsayin shaidu ga Alhaji Musa Imam, hakan ne ya sanya suka biyo shi Kaduna domin tafiya dashi, "shi kuma yana ganin su sai ya fara yi musu ihun barayin mutane, za su sace shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel