Kotu ta tabbatar da nasarar dan majalisar jihar Kano

Kotu ta tabbatar da nasarar dan majalisar jihar Kano

Kotun daukaka kara dake jihar Kaduna, ta tabbatar da nasarar cin zabe ga dan takarar jam'iyyar APC na kujerar majalisar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa, Honarabul Mahmoud Muhammad Santsi.

Yayin yanke hukuncin a wannan mako, kotun daukaka kara a jihar Kaduna, ta shimfida hannayen ta na adalci wajen tabbatar da Honarabul Mahmoud Muhammad Santsi, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa na jihar Kano.

Zauren Majalisar Wakilai

Zauren Majalisar Wakilai
Source: Depositphotos

Da ya ke ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust a garin Abuja bayan samun mallakin takardar shaidar cin zabe daga hannun hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, Honarabul Santsi ya bayar da shaidar yadda tun fil azal ya lashe zaben fidda gwanin takara da tazara mai girman gaske, inda kuma aka sauya sunan sa bayan sakamakon zaben ya isa birnin Abuja.

Yayin bibiyar diddiga da neman hakki tare da samun goyon baya da kuma ingatacciyar shaida ta jam'iyyar APC reshen jihar Kano, kotun daukaka kara bayan gamsuwa da hujjoji ta tabbatar da nasarar Honarabul Santsi inda ta umurci hukumar INEC a kan mallaka masa shaidar cin zabe cikin gaggawa.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 14 a jihar Nasarawa

Legit.ng ta ruwaito cewa, babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Kano ta kwace nasarar dan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Sumaila da Takai, Kawu Sumaila.

Kotun bayan gamsuwa da shaidu da kuma hujjoji ta tabbatar da nasarar Sulaiman Abdulrahman Dambazau, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar tarayya mai wakilcin kananan hukumomin Sumaila da Takai da hakan ya sanya hukumar INEC a makon da ya gabata ta mallaka masa takardun shaidar cin zabe cikin gaggawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel