Wadanda suka yi garkuwa da surukar gwamnan jahar Katsina sun shiga hannu (Hotuna)
Tun bayan da wasu miyagu suka yi garkuwa da surukar gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, watau mahaiyar matarsa, Hajiya Hauwa Yusuf a ranar 8 ga watan Feburairu a gidanta dake garin Katsina, Yansanda suke gudanar da bincike don gano su wa da wa keda hannu cikin satar.
Legit.ng ta ruwaito Allah cikin ikonsa sai gashi kwararren jami’in Dansandan nan kuma dodon duk wani aikata miyagun laifuka, DCP Abba Kyari tare da yaransa sun samu nasarar cafke wadannan gagaruman barayin mutane a jahar Katsina.
KU KARANTA: Mutane 2 sun sheka barzahu bayan gamuwa da ajalinsu a cikin ruwan Kano
Abba Kyari da kansa ya sanar da haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook inda yace ba tare da wata wata ba suka shiga binciken kwakwaf har sai da suka kama barayin, tare da masu basu makamai, da kwayoyi da sauran kayan maye.
Ga sunayen barayin kamar haka:
1) Abdullahi M. Sani 23yrs of Sokoto Rima area of Katsina State,
2) Abubakar Dani mai shekaru 21 dan Sabuwar Unguwa
3) Marwana Gide mai shekaru 25 kauyen yan Maiwa Katsina
4) Rabe Hamza Tankabaje mai shekaru 35 dan kauyen Nasarawa Bugaje
5) Abdulkarim Aliyu mai shekaru 20 dan garin Katsina
6) Musa Yakubu mai shekaru 21 dan garin Katsina
7) Abubakar Abdullahi mai shekaru 25 dan garin of Katsina
8) Napkon Sambo mai shekaru 31 dan Jos
9) Haruna Adamu mai shekaru 31 dan garin Katsina
10) Taiwo Abayomi mai shekaru 28
11) Ali Samaila mai shekaru 45 dan kauyen Mairuwa
12) Abubakar Sulaiman mai shekaru 30 daga kauyen Mairuwa
13) Ibrahim Bille mai shekaru 30 daga kauyen Mairuwa
Dukkanin wadanda aka kama sun tabbatar da hannunsu cikin satar surukar gwamnan, inda suka bayyana yadda yi cinikin kudin fansan da za’a biya, yadda suka karbi kudin da kuma yadda suka raba kudin tsakaninsu, har ma guda daga cikinsu ya kaisu wani sabon shago daya bude a garin Katsina, gidaje da filaye, wanda a yanzu haka duk an kwacesu.
Daga cikin makaman da aka kato daga hannyensu akwai AK 47 guda daya, alburusai da dama, wayoyin mutane da suka kwace da babura biyu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng