'Yan sanda sun harbe Shaho; shugaban gungun masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja

'Yan sanda sun harbe Shaho; shugaban gungun masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewar jami'an atisayen 'Puff adder' sun harbe Sule Shaho, shugaban gungun masu garkuwa da mutane da ya kitsa yin garkuwa da shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC), Dakta Mohammed Mahmood, da diyar sa, Yesmin, a hanyar zuwa Abuja.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce ta kama wasu masu garkuwa da mutane su 7 a cikin sa'o'i 24. Sannan ta ce ta samu nasarar kwace manyan bindigu samfurin AK47 guda 4 da carbi 26 na alburusai.

Da yake bayanin mutuwar Shaho ga manema labarai a Abuja, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mba, ya bayyana cewar ksurgumin dan fashin da ya rikide zuwa garkuwa da mutane ya mutu ne sakamakon raunukan harbin bindigar da ya samu yayin musayar wuta da jami'an 'yan sanda.

Mba ya bayyana cewar Shaho da yaran sa sun dade suna kama mutane tare da yin garkuwa da su a Kaduna da kewaye.

Rundunar 'yan sanda ta harbe wanda ya yi garkuwa da shugaban UBEC yayin musayar wuta
Masu garkuwa da mutane
Asali: Twitter

Mba ya ce an garzaya da Shaho asibiti domin ceto rayuwar sa amma ya mutu a can.

A karshen watan Afrilu ne rahotanni suka bayyana cewar masu garkuwa da mutane sun sako shugaban hukumar ilimin bai daya ta kasa (UBEC), Dakta Mohammed Mahmood, wanda aka sace tare da diyar sa, Yesmin, a hanyar su ta zuwa Abuja.

An sake su ne kwana daya kacal bayan an yi garkuwa da su. Wata majiya ta bayyana cewar sai da iyalin Dakta Mahmood suka bayar da miliyan N13 a matsayin kudin fansa kafin a sake shi tare da diyar sa.

DUBA WANNAN: An kashe sojan Najeriya a kasar Mali

A wancan lokacin, rundunar 'yan sandan ta ce ta kama wani mutum guda dake da alaka da sace Dakta Mahood tare da samun nasarar kwace wata bindiga kirar AK47. Kazalika, ta ce tana gudanar da bincike a kan lamarin.

Masu garkuwa da mutanen sun harbe direban Dakta Mahmood, wanda nan take ya mutu.

Wani shaidar gani da ido, Mohammed Dambatta, wanda ya sha da kyar, ya shaida wa majiyar jaridar cewar masu garkuwa da mutanen sun sace mutane da dama a daidai Kurmin Kare a karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel