Yadda gwamnonin Arewa suka kudirci kawo karshen ta'addanci a yankin

Yadda gwamnonin Arewa suka kudirci kawo karshen ta'addanci a yankin

Gwamononin jihohi 19 da yankin Arewacin Najeriya ya kunsa, sun daura damarar neman kwarewar masana a harkar tsaro domin shimfida tafarki da kuma dabaru na kawo karshen kalubalai na rashin tsaro da suka zamto alakakai a yankin.

Gwamnonin na kuma neman samar da hanyoyin jituwa a tsakanin tanadi na dokoki a kasar domin tabbatar da cewa miyagun ababe masu tayar da barazana da zaman lafiya ba su kauracewa fuskantar hukunci ba.

Gwamnonin Arewa

Gwamnonin Arewa
Source: Twitter

Kungiyar gwamnonin Arewa ta yanke wannan muhimman shawarwari yayin zaman da ta gudanar cikin birnin Kaduna a ranar Juma'ar da ta gabata. Kungiyar ta kafa wani sabon kwamiti domin shimfida tafarki da dabaru na tsarkake yankin Arewa daga ta'adar masu tayar da zaune tsaye.

Ana sa ran wannan kwamiti bisa jagorancin gwamnan jihar Katsina Mallam Aminu Bello Masari, zai samar da muhimman tsare-tsare da kuma tubalin warware matsaloli na rashin tsaro da suka yiwa yankin Arewa dabaibayi.

Kazalika kungiyar gwamnonin za ta nemi ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin shigar da bukatu dangane da halin ni 'ya su ta fuskar rashin tsaro da al'ummomin yankin su ke fuskanta a yanzu.

KARANTA KUMA: Dalibar 'Yan Matan Chibok ta kammala karatun digiri a kasar Amurka

Daya daga cikin gwamnoni yayin ganawar sa da manema labarai, ya ce kungiyar gwamnonin ba za ta lamunci zabin ko wane irin kudiri ba na yafiya ko kuma afuwa ga dukkanin wadanda za a kama da hannu cikin aikata mummunar ta'asa a yankin Arewa.

Bugu da kari kungiyar gwamnonin ta yabawa hukuncin gwamnatin tarayya na haramta hako ma'adanai da albarkatun kasa a jihar Zamfara yayin da ta ke ci gaba da zage dantsen ta wajen inganta harkokin tsaro a yankin Arewa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel