Aikin Umarah: Bidiyon shugaba Buhari yana sassarfa a tsakanin Duwatsun Safa da Marwa

Aikin Umarah: Bidiyon shugaba Buhari yana sassarfa a tsakanin Duwatsun Safa da Marwa

Bayyanar wani faifan bidiyo da ya nuna yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sassarfa cikin karsashi yayin ibada ta aikin Umara a birnin Makkah na kasa mai tsarki, ya sake janyo cecekuce dangane da koshin lafiyar sa.

Aikin Umarah: Bidiyon shugaba Buhari yana sassarfa a tsakanin Duwatsun Safa da Marwa

Aikin Umarah: Bidiyon shugaba Buhari yana sassarfa a tsakanin Duwatsun Safa da Marwa
Source: Twitter

Ko shakka babu kafar watsa labarai ta kasa wato NTA, ta hasko wani faifan bidiyo da ya bayyana yadda shugaban kasa Buhari tare da tawagar sa suka kece cikin sassarfa yayin gudanar da ibada ta aikin Umara a cikin masallaci mai alfarma dake birnin Makka na kasar Saudiya.

Faifan bidiyon ya sake janyo cecekuce tsakanin 'yan adawa da kuma masu goyon bayan shugaban kasa Buhari dangane da koshin lafiyar sa. A baya 'yan adawa da dama sun yi ikirarin cewa, shugaba Buhari ba ya da cikakkiyar lafiya ta cancantar sa wajen jagorantar Najeriya.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Gwamna Bagudu ya nemi hadin kan al'umma a jihar Kebbi

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a bisa tanadi da koyarwa addinin Islama, an hori Maza da suyi sassarfa ta wata 'yar gajeruwar tazara yayin hawa da sauka a tsakanin Duwatsun Safa da kuma Marwa wajen gudanar da ibada ta aikin Hajji ko kuma Umara.

Domin amsa goron gayyata na masarautar kasar Saudiya, shugaban kasa Buhari a ranar Alhamis ya sauka a birnin Madina inda a ranar Juma'a ya gudanar da aikin Umarah tare da uwargidan sa, Aisha Buhari da kuma 'yan tawagar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel