Ndidi ne wanda ya fi kowa tare a Gasar Firimiyan shekarar nan a EPL

Ndidi ne wanda ya fi kowa tare a Gasar Firimiyan shekarar nan a EPL

Mun samu labari cewa ‘Dan wasan tsakiyan nan na Najeriya, Wilfred Ndidi, wanda ke bugawa kungiyar Leicester City, ya zo na farko a cikin jerin ‘yan wasan da su ka fi yin tare a kasar Ingila.

A duk kakar bana, Wilfried Ndidi shi ne ya doke kowane ‘dan wasan tsakiya a Gasar Firimiya wajen yin tare a shekarar nan. Ndidi ya sha gaban manyan ‘yan wasan tsakiya irin su Idrissa Gueye.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, ‘dan kwallon na Super Eagles, Ndidi yayi tare 144 a shekarar nan. Idrissa Gueye shi ne ya zo bayan ‘dan kwallon na Najeriya da yawan tare 143 a kasar Ingila.

KU KARANTA: 'Yan wasan da za su wakilci Najeriya a Gasar Afrika

Ndidi ne wanda ya fi kowa tare a Gasar Firimiyan shekarar nan a EPL
Ndidi yana 'yan wasan da su ka fi kowa tare a tsakiya
Asali: Getty Images

Wanda kuma ya zo na uku a jerin shi ne ‘dan wasa Aaron Wan-Bissaka. Tsohon ‘dan wasan kungiyar Genk, Matashin ‘dan wasa Wan-Bissaka, yayi tare har 128 bayan ya dawo Ingila da kwallo.

A shekarar bara, ‘Dan wasan na Najeriya shi ne ya doke kowa wajen iya tare a Ingila, inda ya kai tokari har 138 a kakar 2017. A tarihin Firimiya, ba a taba samun wanda yayi irin wannan fice ba.

Idan ba ku manta ba, Ndidi ya shiga cikin Tawagar Zakarun Matasan da su ke buga wasa a Ingila a shekarar bara. An yi la’akari da kokarin ‘dan kwallon tsakiyan ne wajen wannan sa shi a wannan sahu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel