Najeriya da Nijar za suyi hadin gwiwa don yaki da 'yan bindiga

Najeriya da Nijar za suyi hadin gwiwa don yaki da 'yan bindiga

- An gudanar da taro na musamman tsakanin hukumomin tsaron na Najeriya da takwarorinsu na Nijar a garin Dakana domin magance hare-haren 'yan bindiga

- Taron ya samu hallarcin wakilan jami'an tsaro daga rundunar sojojin Najeriya, 'Yan sandan Najeriya, 'Yan sandan farar hula, DSS, Jami'an Immigration, Jami'an Kwastam da kuma Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC

- An tattaunawa muhimman batutuwa da za su taimakawa wurin inganta sintiri a kan iyakokin kashashen biyu tare da magance hare-haren 'yan bindiga a jihar Sokoto da kewaye

Wata tawagar jami'an tsaro na hadin gwiwa daga Najeriya sun hadu da takwarorinsu daga Jamhuriyar Nijar a Dakana na kasar Nijar domin tattauna yadda za su inganta tsaro a kan iyakan kasashensu da niyyar magance 'yan bindiga.

Najeriya da Nijar za suyi hadin gwiwa don yaki da 'yan bindiga

Najeriya da Nijar za suyi hadin gwiwa don yaki da 'yan bindiga
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda masu ciwon Ulcer za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana

Tawagar jami'an tsaron daga Sokoto sun hada da Jami'an sojojin Najeriya, 'Yan sandan Najeriya, 'Yan sandan farar hula, DSS, Jami'an Immigration, Jami'an Kwastam da kuma Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC.

Mukadashin mataimakin jami'in hulda da jama'a na sojojin Najeriya, Kwanel Sagir Musa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Juma'a a Sokoto inda ya ce: "Wakilan Najeriya sun tattauna da takwarorinsu na Nijar kan hanyoyin da za su bi domin tunkarar kallubalen tsaro a jihar Sokoto da kewaye."

Ya ce barazanar tsaron da ake samu a kan iyakan Najeriya da Jamhuriyar Nijar ne ya yi sanadiyar kafa tawagar hadin gwiwa na sojoji da ke sintiri a kan iyakokin kasar a Satumban 2018.

Ya cigaba da cewa Brig. Janar LKN Udeagbala ne ya wakilci kwamandan Division 8, Brigade 1 na dakarun Sojojin Najeriya wanda ya jagoranci tawagar ta Najeriya a wurin taron inganta tsaron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel