Shauki ya kama Buhari yayin daya kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah (Hotuna)

Shauki ya kama Buhari yayin daya kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Saudiyya bisa gayyatar mai alfarma Sarkin Saudiyya Sarki Salman dan Abdul Aziz domin ya gudanar da ibadar aikin Umarah, inda a daren jiya Alhamis ya samu kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis ne jirgin shugaban kasa ya shilla kasar Saudiyya dauke da shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan mukarrabansa, inda ake sa ran zasu dawo gida Najeriya a ranar Talata 21 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Mummunan hatsarin jirgin sama ya faru a kasar Dubai, mutane 4 sun sheka barzahu

Shauki ya kama Buhari yayin daya kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah (Hotuna)
Buhari a kabarin Annabi
Asali: Twitter

A cewar kaakakin shugaban kasa, Garba Shehu, wannan shine karo na biyu da Sarkin Saudiya ya gayyaci Buhari zuwa kasarsa domin yin Umara, amma Buhari yaki amsa gayyata a bara, sai a bana ne ya amsa gayyatar Sarki Salmanu.

Saukan jirgin Buhari keda wuya sai ga mataimakin gwamnan Madinah, Yarima Saud bin Khalid Al-Faifal yana jiransa, inda ya bashi kyakkyawar tarba a matsayinsa na babban bakon Sarki Salmanu, kai tsaye Buhari ya wuce Masallacin Annabi dake Madinah.

Shauki ya kama Buhari yayin daya kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah (Hotuna)
Buhari a kabarin Annabi
Asali: Twitter

A wannan Masallaci ne Buhari ya gudanar da sallar Magriba, Isha’I da kuma sallolin nafilar Tarawihi bayan ya sha ruwa, sa’annan daga bisani ya garzaya kabarin Annabi Muhammadu inda ya kai gaisuwa.

An hangi tsaurara matakan tsaro da gwamnatin kasar Saudiyya ta zuba don tsaron shugaba Buhari a zaman da zai yi a kasar, sakamakon yadda Sojojin askar suke zagayeshi a duk inda ya shiga, tare da bashi kariya daga cudanya da sauran mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng