Maganganu masu ratsa zuciya da Zainab Aliyu ta yi bayan dawowar ta gida Najeriya daga Saudiyya

Maganganu masu ratsa zuciya da Zainab Aliyu ta yi bayan dawowar ta gida Najeriya daga Saudiyya

Bayan dawowar ta daga kasar Saudiyya inda aka kamata da zargin amfani da miyagun kwayoyi, Zainab Aliyu ta yi hira da manema labarai inda ta ke bayyana irin halin ha'ula'in da ta shiga a lokacin da jami'an tsaron kasar Saudiyya suka kamata

Ga irin hirar da ta yi da manema labaran cikin kuka da ban tausayi, dan jaridar ya fara tambayarta yadda lamarin ya faru har aka kai ga kamata,ga amsar da ta ba da:

Maganganu masu ratsa zuciya da Zainab Aliyu ta yi bayan dawowar ta gida Najeriya daga Saudiyya
Maganganu masu ratsa zuciya da Zainab Aliyu ta yi bayan dawowar ta gida Najeriya daga Saudiyya
Asali: Facebook

Ina tare da mahaifiyata da yayata a daki a masaukinmu na Madina, muna kwance kawai sai aka shigo aka sanar dani ga abinda nayi, ni kuma ban san komai a cikin wannan lamari ba.

Su wanene suka sanar da ke, kuma ta yaya suka tinkare ki?

Jami'an tsaronsu ne suka zo cikin farin kaya, suka tashe ni suka fada min abinda na yi.

Yaya aka yi har suka kai inda kike har suka nuna ki?

Lokacin bacci na kai na ban ma san me suke yi ba, amma ganin sun fito da ankwa sun sanya mini, sai hankalina ya dawo jikina, na fara tunanin wai menene nayi ake kokarin kamani.

A rayuwarki an taba saka miki ankwa ne?

Ni tunda nake ban ma taba ganinta da idona ba sai ranar.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Hukumar gidan yari da hukumar kashe gobara za su dauki ma'aikata dubu 10

Wane irin tashin hankali kika shiga lokacin da aka raba ki da mahaifiyarki da yayarki?

Allah ne kadai yasan irin tashin hankalin dana shiga, saboda bazan iya misalta shi ba. Saboda da suka gama yi min tambayoyi sai suka dauke ni daga Madina suka kai ni Jidda. A lokacin babu abinda ke raina irin mahaifiyata, saboda kowa na gani kokarin da nake ya bani waya na kira mahaifiyata.

Ko zaki iya fada mini yaya rayuwar gidan yarinsu ta ke?

Babu abinda zan iya cewa akan rayuwar wurin, saboda dana je gurin naga babu mai iya taimakona sai Allah, kawai sai na dage da addu'a akan Allah ya fitar dani daga wannan kangi da nake ciki.

Shin yaya daren farko ya kasance miki a gidan yari?

An ce akwai daren da mutum baya iya ko runtsawa, amma ance akwai barawon bacci, to ni gaskiya barawon baccin ma bai zo mini ba.

A gurin wa kika samu labarin cewa an wankeki daga laifinki zaki fito?

Ban ji labari a gurin kowa ba, kawai ranar da zan fito dinne aka ce mini zan fito, sai naga mutane ana shigowa ana taya ni murna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel