Shugaban karamar hukuma a Katsina ya koka akan lamarin tsaro

Shugaban karamar hukuma a Katsina ya koka akan lamarin tsaro

- Alhaji Mannir Muazu, ya koka akan tabarbarewar lamarin tsaro a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina

- Muazu wanda ya kasance Shugaban kasaramr hukumar yace lamarin rashin tsaro na dada bunkasa duk da tari jami’an tsaro da aka tura yankin

- Shugaban karamar hukumar ya kuma yi kira ga mutane da su jajirce wajen addu’a a yayin azumin Ramadan domin su nemi doki a wajen Allah

Shugaban karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina, Alhaji Mannir Muazu ya koka akan tabarbarewar tsaro a yankin, cewa mazauna yankin basu da kwanciyar hankali.

Ya fada wa manema labarai a ranar Talata, 14 ga watan Mayu, a Batsari cewa matakin rashin tsaro a yankin na karuwa a kullun duk da kasancewar jami’an tsaro da aka tura yankin.

“Muna fuskantar matsalar rashin tsaro a yankin; muna cikin mawuyacin hali,” inji Muazu.

Shugaban karamar hukuma a Katsina ya koka akan lamarin tsaro

Shugaban karamar hukuma a Katsina ya koka akan lamarin tsaro
Source: UGC

Ya bukaci mutane da su nemi hanyoyin kare kansu daga harin yan bindiga.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya kafa kwamitin kaddamar da mafi karancin albashi

Ya bayyana cewa akwai bukatar yin wannan kira saboda lamarin na iya shafar noma yayinda yan bindiga ke barazanar kai hari gga manoma a gonaki lokacin girbe albarkatun noma.

Shugaban karamar hukumar ya kuma yi kira ga mutane da su jajirce wajen addu’a a yayin azumin Ramadan domin su nemi doki a wajen Allah

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel