Zababben Gwamnan Gombe ya kafa kwamitin mutum 30 na karbar ragamar mulki

Zababben Gwamnan Gombe ya kafa kwamitin mutum 30 na karbar ragamar mulki

Zababben gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya kafa kwamitin mutum talatin da za su jagoranci ragamar harkokin rantsuwa da kuma karbar akalar sabuwar gwamnatin sa a jihar.

Zababben Gwamnan Gombe ya kafa kwamitin mutum 30 na karbar ragamar mulki
Zababben Gwamnan Gombe ya kafa kwamitin mutum 30 na karbar ragamar mulki
Asali: UGC

Kwamitin bisa jagorancin Sanata Joshuwa Lidani zai hadar da Alhaji Abubakar Mu'azu a matsayin mataimakin jagoran kwamitin yayin da Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo Waziri zai kasance sakataren sa.

Da ya ke dai ance ba a fafe gora ranar tafiya, Alhaji Inuwa yayin kafa kwamitin a karshen makon da ya gabaa yace hakan ya bayu ne domin tumke damara ta tabbatar da inganci wurin karbar akalar jagoranci gami da aminci yayin bikin rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya nemi mambobin kwamitin da su hada gwiwa da kwamitin da gwamnan jihar mai barin gado ya kafa, Ibrahim Hassan Dankwambo domin tabbatar da nasarar karba da kuma mika akalar jagoranci ta gwamnatin jihar Gombe.

KARANTA KUMA: JAMB ta mayar da N5bn asusun gwamnatin tarayya

Sauran manyan mambobin kwamitin sun hadar da; John Lazarus Yoriyo, Mista Amangal Nite, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali, Khamisu Ibrahim Mai Lantarki, Aishatu Jibir Dukku, Alhaji Danjuma Babayo Kwadon, Alhaji Sunusi Ataka, Naomi Awak, Vasty Saleh, Alhaji Abubakar Adamu, Alhaji Abubakar Kari, Julius Ishaya da sauran su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel