Domin na kasance jakadan zaman lafiya ya sanya zan hakura da kujerar Sanata - David Mark
Mun samu rahoton cewa tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark, ya yi karin haske na fayyace dalilan sa na hakura da kujerar Sanata tare da janye jiki daga zauren majalisar tarayyar kasar nan.
Sanata David Mark ya ce domin ya zamto jakadan zaman lafiya ga mahaifar sa da kuma kasar Najeriya baki daya, ya sanya zai dasa aya ta hakura da kujera a zauren majalisar dattawan kasar nan.
Tsohon shugaban majalisar ya bayyana hakan ne yayin halartar taron addu'o'i na mako-mako da aka gudanar cikin babban cocin Katolika na Augustine da ke yankin Otukpo na jihar Benuwai a ranar Lahadin da ta gabata.
Sanata Marka wanda ya shafe tsawon shekaru 20 a zauren majalisar dattawan kasar nan, ya kwarara yabo gami da jinjina ga al'ummar mazabar sa a sanadiyar samun goyon baya maras yankewa a tsawon shekarun da ya shafe yana wakilcin su.
Ya mika kokon barar sa a gare su na neman yafiya akan duk wasu kura-kurai ko kuma ba daidai ba da ya aikata yayin rike akalar jagoranci tsawon shekaru ashirin da ya shafe a zauren na majalisar tarayya.
KARANTA KUMA: Mahaifin zababben mataimakin gwamnan jihar Legas ya riga mu gidan gaskiya
Cikn na sa jawaban, gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi yabo ga tsohon shugaban majalisar dattawan kasar nan tare da misalta shi a matsayin madubin dubawa ga al'umma da ya tubali na gaskiya da sadaukar wa wajen yiwa jihar sa hidima.
Kazalika tsohon Ministan harkokin cikin gida Abba Moro, wanda zai maye gurbin Sanata Mark a zauren majalisar dattawan Najeriya, ya ce tsohon shugaban majalisar ya yi tsayuwar daka ta rike amana da kuma aminci na gaskiya da al'ummar jihar Benuwai suka rataya a wuyan sa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng