Wasanni 5 da suka sanya Manchester City ta lashe gasar Firimiya a bana

Wasanni 5 da suka sanya Manchester City ta lashe gasar Firimiya a bana

A Yammacin yau na Lahadi, 12 ga watan Mayun 2019, aka karkare wasannin gasar cin kofin firimiya na bana a Ingila. Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce ta sake lashe gasar karo na biyu a jere kenan ba tare da wata kungiyar ta iya lakace ma ta hanci ba.

Wasanni 5 da suka sanya Manchester City ta lashe gasar Firimiya a bana
Wasanni 5 da suka sanya Manchester City ta lashe gasar Firimiya a bana
Asali: Twitter

Bayan lallasa kungiyar Brighton Albion ci hudu da daya, kungiyar Manchester ta sha da kyar na lashe gasar firimya da maki daya rak a tsakanin ta da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke biye a bayan ta.

Shafin wasanni na jaridar AFP ya bayyana cewa, akwai wasu manyan wasanni biyar da suka taka rawar gani wajen dankawa kungiyar Manchester City nasara a bana wanda fitaccen mai horas da 'yan wasa ke rike da ita wato Pep Guardiola.

KARANTA KUMA: A shekarar 2023 zan janye jiki daga majalisar dattawa - Ekweremadu

Ga jerin manyan wasanni biyar da suka sanya kungiyar Manchester City ta zamto zakara a bana kamar haka;

Manchester City 2 - Liverpool 1

Manchester City 6 - Chelsea 0

Manchester City 1 - Tottenham 0

Manchester United 0 - Manchester City 2

Manchester City 1 - Leicester City 0

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng