Miyagu sun kai hari a Garin Sabon Birni sun hallaka jama’a

Miyagu sun kai hari a Garin Sabon Birni sun hallaka jama’a

Labari maras dadi ya zo mana cewa wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a gano su ba, sun shiga cikn wasu Kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, inda su ka kashe mutane da-dama.

Gidan Talabijin na TVC News ya rahoto cewa an shiga Kauyukan da ke cikin yankin Sabon Birni, an kashe mutane. Har yanzu dai ba a samu takamaimen adadin jama’an da aka kashe a wannan mummunan hari da aka kai ba.

Kamar yadda rahotanni ke zuwa mana daga cikin Kauyen Gatawa, mutanen yankin su tsere sun shiga cikin kasar Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka. Mutane da-dama sun samu rauni wanda yanzu haka su na kan gadon asibiti.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun yi ram da masu garkuwa da mutane

Miyagu sun kai hari a Garin Sabon Birni sun hallaka jama’a

Sufeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu
Source: UGC

Dakarun da aka tura zuwa cikin karamar Sabon Birni, sun yi ta faman artabu da wadannan ‘yan bindiga wanda wannan karo ya jawo mutuwa da raunin Bayin Allah da dama. Daga cikin wadanda aka yi wa rauni har da wasu Sojojin kasar.

Wadannan Sojoji 3 da su ka samu rauni a sanadiyyar harin su na cikin wani asibiti ana kula da su. Har yanzu dai ba mu samu wani karin bayani a game da wannan hari ba, amma babu shakka an ce ‘yan bindigan sun yi mugun ta’adi.

Sai dai jami’an ‘yan sanda sun ce ba su san da labarin wannan hari ba. Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Mohammed Abubakar Sadiq, yace za su yi wani abu daga sun samu labari ya kai gare su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel