Daga fadar gaskiya: Ban ga wani laifin da Mahaifina yayi ba inji Adam Sanusi II

Daga fadar gaskiya: Ban ga wani laifin da Mahaifina yayi ba inji Adam Sanusi II

Kamar yadda labari ya zo mana, Yaron Sarki Muhammad Sanusi II watau Adam Lamido Sanusi (wanda aka fi sani da Ashraf), ya fito yayi magana a kan rikicin da ya barke tsakanin Mahaifinsa da kuma gwamna Abdullahi Ganduje.

Kwanan nan ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya raba masarautar Kano zuwa gidaje 4 inda ya fitar da manyan Sarakuna a Gaya, Rano, Karaye da kuma yankin Bichi daga cikin fadar Sarki Muhammadu Sanusi na II.

Adam Lamido Sanusi ya fito yayi magana yana addu’a Ubangiji ya taimaki duk wanda yake kan daidai tsakanin Mahaifinsa Mai martaba Sanusi II da kuma gwamna Abdullahi Ganduje. Adam ya fadi wannan ne a shafin sa na Instagram.

Ga abin da Yaron Sarkin ya fada:

“Tsakanin Sarki da Gwamna, duk wanda yake kan daidai, mu na addu’a ya samu nasara. Mahaifina ya kan fadi duk abin da yake cikin ran sa a lokacin da yake ganin ya dace, kuma sam ban ga wani laifi a kan yi hakan ba…”

KU KARANTA: Yadda aka tsige Sarkin Kano Sanusi I shekaru 50 da su ka wuce

Daga fadar gaskiya: Ban ga wani laifin da Mahaifina yayi ba inji Adam Sanusi II

Gwamnan Kano ya kacancana Masarautar Jihar Kano
Source: Twitter

Ashraf Sanusi II ya kara da cewa:

“Idan har aka tsige shi (Sarki) ko kuma a rage masa matsayi, zan yi wa al’umma su samu shugaba adali mai gaskiya kamar sa... “

Yaron na Sarki yake cewa bai kamata mutane su rika fitowa su na zagin manya a kan wannan batu ba inda yace:

“Ni ba masani bane a harkar siyasa ko zamantakewar jama’a, a kashin gaskiya, ina godewa masu goyon bayan Mahaifina, amma ina kira ga Masoya su guji sukar wani a lokacin da su ke bayyana ra’ayinsu.”

Yaron Sarkin ya kuma cigaba da cewa:

“A guji aikin gaggawa ba tare da fahimtar ainihin abin da yake wakana ba. Ka da kuma mu dauki karon tsana mu daurawa wani, saboda son rai.”

A karshe, a jawabin na Adam Lamido Sanusi a shafin yanar gizo, yayi kira ga jama’a su kyale wannan rikici tsakanin manyan kasa masu ilmi, domin su ne su ka fi kwarewa a kan sha’anin mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel