2019: James Falake zai nemi tikitin APC a hannun Gwamnan Kogi

2019: James Falake zai nemi tikitin APC a hannun Gwamnan Kogi

A daidai lokacin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yake fitowa yana tabbatar da cewa zai nemi tazarce a zaben 2020, mun ji labari cewa an fara samun wasu da ke harin kujerar ta sa a jihar.

James Faleke wanda yayi takara a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kogi a zaben 2016, ya dawo da karfin sa wannan karo inda yake sa ran cewa zai karbe tikitin APC daga hannun Yahaya Bello domin neman gwamnan Kogi.

Labarin da mu ke ji shi ne tuni har fastocin James Falake a karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun fara yawo a gari. Hotunan tsayawa takarar ‘dan majalisar sun shiga har cikin babbar sakatariyar jam’iyyar APC da ke birnin Abuja.

KU KARANTA: Gwamna Yahaya Bello ya gana da Tinubu domin samun tikitin APC

2019: James Falake zai nemi tikitin APC a hannun Gwamnan Kogi
‘Dan Majalisar Legas zai yi takara da Yahaya Bello a zaben Kogi
Asali: Twitter

Yanzu haka James Faleke, ‘dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Ikeja a majalisar tarayya a karkashin APC mai mulki, amma asalinsa mutumin jihar Kogi ne. Faleke shi ne Abokin takarar Marigayi Prince Abubakar Audu a zaben 2015.

Idan ba ku manta ba, Abubakar Audu ya rasu ne a lokacin da ake daf da karasa zaben gwamna a jihar Kogi. Wannan ya sa Faleke ya nemi INEC ta bayyana sa a matsayin wanda zai zama gwamna, amma INEC ta zabi Yahaya Bello.

Yahaya Bello shi ne ya zo na biyu wajen zaben fitar-da-gwani na zaben gwamna da APC ta shirya a jihar Kogi a tsakiyar 2015. Yanzu dai Faleke ya dawo da nufin karbe mulkin jihar daga hannun gwamna mai ci zaben Nuwamban bana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel