Gwamna Nasir El-Rufai bai nufi ci wa Bola Tinubu mutunci ba – APC

Gwamna Nasir El-Rufai bai nufi ci wa Bola Tinubu mutunci ba – APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta reshen Kaduna tayi wuf ta fito ta kare Gwamnan jihar watau Malam Nasir El-Rufai a kan jawaban da ya fito yayi kwanaki lokacin da ya kai ziyara zuwa Legas kwanan nan.

Gwamnan yayi jawabi a kan yadda za ayi maganin siyasar Uban gida a Najeriya, wanda wasu ke ganin cewa Nasir El-Rufai yana habaici ga tsohon gwamnan Legas kuma babban jigo a cikin jam’iyyar APC watau Bola Tinubu.

Jam’iyyar APC ta jihar Kaduna tayi karin-haske a Ranar Larabar nan, 9 ga Watan Mayu. Jam’iyyar tace babu abin da ya hada jawaban da gwamnan ta yayi, da kuma caccakar Bola Tinubu wanda jigon APC ne a Kudancin Najeriya.

APC tayi wannan jawabi ne ta bakin Salisu Tanko Wasuno, wanda shi ne mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar a Jihar Kaduna. Tanko Wasuno yace abin da gwamnan yake magana a kai shi ne kira ga jama’su rika yin zabe.

KU KARANTA: Jigon APC ya nemi Buhari ya guji aiki da masu fuska-biyu a 2019

Gwamna Nasir El-Rufai bai nufi ci wa Bola Tinubu mutunci ba – APC

Ana ce-ce-ku-cen El-Rufai ya dura a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Wasuno yake cewa wasu sun yi wa maganar da gwamna El-Rufai yayi wata irin mummunar fassara inda yace a cikin mutum miliyan shida da ake da su a jiha, bai fi mutum miliyan guda ne kurum su ke fitowa a ranar da ke yin zabe.

Tanko Wasuno ya kara da cewa a matsayin su na jam’iyya, dole su fito su kare gwamnan su, ganin yadda APC ta bangaren Legas ta dauki maganar gwamnan a bai-bai. APC tace abin da Gwamnan yake yi kira ne ga masu zabe ba komai ba.

APC ta tabbatar da cewa binciken da tayi bayan ta zauna da wadanda abin ya shafa, ta gano cewa ko kadan gwamnan bai ci mutuncin Tinubu ba, illa iyaka yayi magana ne a kan yadda ya casa wasu manyan ‘yan siyasan Kaduna a zaben 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel