Hanyar Abuja zuwa Kaduna ita ce hanya mafi hadari a fadin nahiyar Afirka

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ita ce hanya mafi hadari a fadin nahiyar Afirka

- Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin hanyar da tafi kowacce hanya hadari a nahiyar Afirka

- Sanatocin sun ce dolene gwamnati ta tashi tsaye wurin karo jiragen kasa da za su isa yin jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna

Yau ne majalisar dattijai ta Najeriya ta bayyana babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a matsayin hanya mafi hadari a nahiyar Afirka, saboda matsalar masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami da suka addabi matafiya da suke bin hanyar.

Sai dai abinda dakin majalisar ya bayyana ya sha banban da abinda shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Mohammed Adamu wanda ya tabbatarwa da matafiya masu bin hanyar cewa yanzu komai ya dawo daidai.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ita ce hanya mafi hadari a fadin nahiyar Afirka

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ita ce hanya mafi hadari a fadin nahiyar Afirka
Source: Depositphotos

Sanata Shehu Sani, yayin da yake tofa albarkacin bakin shi akan matsalar ya ce, "Ana bukatar a kara yawan jiragen da suke zuwa Abuja da Kaduna cikin gaggawa," inda ya bayyana babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a matsayin hanyar da tafi kowacce hanya hadari a Afirka.

Sanata James ya ce hanyar ba wai hanya ce marar hadari kawai ba, hanya ce da tafi kowacce hanya hadari a Afirka.

Dan majalisar dattawa na jihar Delta ta tsakiya ya bayyana cewa duk mutumin da ya bi hanyar a wannan lokacin to kamar ya kai kanshi gidan mutuwa ne.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Akwai yiwuwar tafiya yajin aiki a fadin Najeriya

Sanata Shehu Sani ya ce dole ne gwamnati ta dauki nauyin makera domin su fara kera sababbin jirage.

Hakazalika shi ma Sanata Bala Ibn Na'Allah da ke jihar Kebbi ya ce abinda ya kamata gwamnatin tarayya ta yi shine ta kara yawan jirage da suke zirga zirga daga Abuja zuwa Kadunan.

A karshen tattaunawar ta su dai sun yanke hukuncin tsayawa domin kawo mafita ga matsalar.

Sannan sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara yawan jiragen kasa da suke bin hanyar Kaduna zuwa Abujan wanda za su isa jigilar fasinjoji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel