Bayan 'sa hannun' Ganduje: Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5

Bayan 'sa hannun' Ganduje: Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sabbin masarautu guda hudu (4) da suka hada da Rano, Karaye, Gaya da Bichi.

Bayan saka hannu a kan wannan sabuwar doka, gwamnatin Jihar Kano zata nada sabbin sarakuna na wannan masarautun hudu da kuma zana iya fadin kasar su, sannan kuma shi Sarkin Kano na yanzu Mallam Muhammadu Sanusi II zai zama Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.

Sarkin Birni da Kewaye na da kananen hukumomi guda 10 a karkashin sa da suka hada da

1- Kano Municipal

2- Fagge

3- Nasarawa

4- Gwale

5- Tarauni

6- Dala

7- Minjinir

8- Ungogo

9- Kumbotso

10- Dawakin Kudu

Bayan 'sa hannun' Ganduje: Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5

Sarki Sanusi II da Ganduje
Source: Twitter

Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1- Rano

2- Bunkure

3- Takai

4- Kibiya

5- Sumaila

6- Doguwa

7- Kiru

8- Bebeji

9- Kura

10- Tudun Wada

Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1.Gaya

2.Ajingi

3.Albasu

4.Wudil

5.Garko

6.Warawa

7.Gezawa

8.Gabasawa

DUBA WANNAN: Jabun kaya: 'Yan sanda sun kama wani dan Chana a Kano

Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1- Bichi

2- Bagwai

3- Shanono

4- Tsanyawa

5- Kunci

6- Makoda

7- Danbatta

8- Dawakin Tofa

9- Tofa

Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1- Karaye

2- Rogo

3- Gwarzo

4- Madobi

5- Kano

6- Rimin Gado

7- Garun Mallam

Sarkin Birnin Kano da Kewaye Mallam Muhammadu Sanusi II shine zai zamu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakin sa. Sannan shugabancin wannan majalisar zai zamu na karba karba ne wato rotational inda kowanne shugaba zai shekara biyu inda bayan kammalawar waainda sa kuma gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani waadin karo na biyu.

Sannan sauran yan majalisar masarautar sun hada da

1- Sakataren Gwamnatin Jiha

2- Kwamishinan Kananen Hukumomi

3- Ciyamomin Mulki na kananen hukumomin

4- Hakimai masu nada Sarki bibiyu saga kowacce Masarauta.

5- Wakilcin mutum 5 da Gwamna zai nada.

Daga karshe kuma sabuwar dokar bata hana wani wanda ya gaji Sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu ba, zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye indai har sun gada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel