Malaman makarantun Firamari 450 sun samu karin girma a jahar Kano
Akalla Malaman makarantun Firamari dari hudu da hamsin ne suka samu karin girma a karamar hukumar Kura ta jahar Kano, kamar yadda sakataren ilimin karamar hukumar, Sulaiman Danjuma-Kura ya bayyana.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sulaiman Kura ya bayyana haka ne a ranar Talata, 7 ga watan Mayu, inda yace karamar hukumar ta kara ma Malaman Firamri 450 girma a cikin watanni goma sha takwas da suka gabata.
KU KARANTA: Abin kunya: An kaure da dambe a zauren majalisa, an karairaya sandan iko
Sulaima yace an kara ma Malaman girma ne domin hakan ya kara musu kwazo tare da basu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu, wanda hakan ke nuna ana sane da irin gudunmuwar da suke bayarwa ga cigaban ilimi.
“Mun amince da karin girma ga Malaman Firamari, a yanzu haka Malamai 450 sun samu wannan karin matsayi.” Inji shi. Sakataren Ilimin ya kara da cewa karamar hukumar zata bada fifiko ga jin dadin Malamai da walwalarsu.
Bugu da kari a yanzu haka sakataren yace sun kafa wata makarantar Firamari ta kimiyya a garin Dan Hassan don habbaka ilimin kimiyya a makarantu, tare da sanya ma daliban Firamari sha’awar karantar kwasakwasan kimiyya a manyan makarantu.
Daga karshe yace sun horas da Malamansu akai akai don samun kwarewa akan sabbin hanyoyin koyarwa na zamani, haka zalika suna bayar da ilimin Firamari dana karamar sakandari kyauta ga marayu a yankin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng