Jihar Borno ta yiwa wasu jihohin Najeriya 6 zarra ta samun kudaden shiga

Jihar Borno ta yiwa wasu jihohin Najeriya 6 zarra ta samun kudaden shiga

Duk da fama da kalubalai na rashin tsaro, jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta yiwa wasu jihohi shida da ke fadin kasar nan fintinkau ta fuskar samar da kudaden shiga a sanadiyar kwazon gwamnatin ta.

Cikin sabon rahoton da aka fitar a kwana-kwanan, jihar Borno da ke ci gaba da fuskantar kalubalai na aukuwar hare-hare ta yi kwazon gaske wajen samar da kudaden shiga fiye da na wasu jihohi shida a fadin kasar nan cikin shekarar 2018 da ta gabata.

Gwamnan Jihar Borno; Kashim Shettima
Gwamnan Jihar Borno; Kashim Shettima
Asali: Facebook

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a mkon da ya gabata hukumar fidda kididdiga ta kasa NBS, National Bureau of Statistic, ta bayyana rahoton adadin kudaden shiga da jihohin kasar nan suka samu a bara cikin shafin ta na yanar gizo.

A yayin da jihar Borno ta samu kudaden shiga na kimanin Naira Biliyan 6.52 a bara, kididdigar ta bayyana cewa, jihohin sun samu tarin kudaden shiga ta hanyar karbar haraji a kan kowane mai daukan albashi, harajin tituna da kuma na ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati.

Cikin jihohi da jhar Borno ta sha gaban su wajen samun kudaden shiga sun hadar da makotan ta biyu, jihar Adamawa da kuma Yobe da ke tarayya da ita wajen ci gaba da fama da kalubalai na ta'addanci.

KARANTA KUMA: Messi zai kai har shekaru 45 kafin ya daina buga tamola - Bartomeu

A yayin da jihar Adamawa ta samu kudaden shiga na kimanin Naira Biliyan 6.20, jihar Yobe ta samu Naira Biliyan 4.38 na kudaden shiga a shekarar 2018 da ta gabata.

Sauran jihohin da jihar Borno ta yiwa zarra ta fuskar samar da kudaden shiga sun hadar da; Ekiti (N6.47bn), Ebonyi (N6.14bn), Taraba (N5.97bn) da kuma jihar Kebbi (N4.88bn).

Kididdigar da hukumar NBS ta fitar ta haskaka cewa, jihar Legas ta yiwa sauran jihohin Najeriya fintinkau yayin da ta samar da kudaden shiga na kimanin Naira Biliyan 382.18. Jihar Ribas ta biyo bayan ta da Naira Biliyan 112.78.

Sauran jihohin da suka yi kwazo sun hadar da; Ogun (N84.55bn), Delta (N58.44bn) sai kuma jihar Kano (N44.11bn).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel