Ramadana: Abubuwa 5 da aka haramta ma duk wani Azumi

Ramadana: Abubuwa 5 da aka haramta ma duk wani Azumi

A daren Lahadi, 5 ga watan Mayu ne mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da fara azumin Ramadana, inda yace sun samu labarin ganin sabon watan Ramadana a jahohin Yobe, Sokoto da Kebbi.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da 1 ga watan Ramadana ne Musulman duniya suka dauki azumi dake alanta shiga watan Azumin Ramadana, watan da Allah mai girma da daukaka Ya saukar da Al-Qur’ani.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnan Kano ya fara kulle kullen tsige Sarkin Kano

Da wannan ne muka kawo muku wasu muhimman abubuwa guda biyar da addinin Musulunci ya bukaci duk wani Musulmi ya kaurace ma aikatasu, kamar;

1- Shan giya, sigari da miyagun kwayoyi

Akwai bukatar Musulmai su nisanci shan giya da duk wasu kayan maye a yayin da suke azumin watan Ramadan don kauce ma illata rayuwarsa.

2- Saduwa da iyali da tsakar rana

Ya kamata mai Azumi ya kauce ma saduwa da iyalinsa a Ramadan, musamman da rana, yayin da bakuna ke kulle, amma an halasta saduwa da iyali da dare.

3- Yasashshen magana

Duk wani zance da ba zai amfanar da mutum ko mai sauraronsa ba, bai kamata aji yana fita daga bakin mai Azumi ba, kamata yayi mai Azumi ya kasance yana yawaita ambaton Allah da karatun Qur’ani.

4- Yawan barci da lalaci

An bukaci Musulmai su kasance sun yi amfani da kowanni dakika na want Ramadan wajen aikin bauta da duk wata ibadar da zata kusantar dasu ga Allah domin samun lada da kyakkyawar makoma, don haka ake kira ga mai azumi ya kiyayi yawan barci kamar kasa da nuna lalaci.

5- Zinace zinace da kallon fina finan batsa

Kalle kallen duk wani abinda zai tayar da sha’awa ko aikata zina ba na mai azumi bane, saboda idan har mai azumi ya fitar da maniyyi sakamakon ire iren wannan kalle kalle ko ma zinar kanta, tabbas Azumi ya karye, sai mutum yayi kaffara bayan watan Ramadana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng