Tsawon lokacin da mutane ke yi da azumi a bakin su a kasashen duniya

Tsawon lokacin da mutane ke yi da azumi a bakin su a kasashen duniya

Lokacin azumi na daya daga cikin lokuta mafi muhimmanci ga al'ummar Musulmi na duniya, lokaci ne da daukacin Musulman duniya ke kara mayar da kai wurin yin ibada domin kusanta kai, da kuma neman yardar Allah (SWT)

A binciken da majiyarmu LEGIT.NG ta gabatar ta gano cewa kasashen da suke yankin tsakiyar duniya, wadanda aka fi sani da 'Equator' a turance sun fi samun gajeren lokacin gabatar da azumi, amma kuma kasashen da suke yankin arewacin duniya su na dadewa sosai kafin ace rana ta fadi, hakan na faruwa ne saboda tsawon yinin da al'ummar yankin suke fuskanta a lokacin zafi.

Tsawon lokacin da mutane ke yi da azumi a bakin su a kasashen duniya
Tsawon lokacin da mutane ke yi da azumi a bakin su a kasashen duniya
Asali: UGC

Ga jerin kasashen duniya da tsawon sa'o'in da suke shafewa su na yin azumi a wannan wata mai alfarma:

Kasa Sa'a

1. Australia 12

2. Chile 12

3. South Africa 12

4. Brazil 13

5. Indonesia 13

6. Kenya 13

7. Nigeria 13

8. Tanzania 13

9. Saudi Arabia 14

10. Senegal 14

11. Afghanistan 15

12. Egypt 15

13. India 15

14. Libya 15

15. Morocco 15

16. China 16

17. USA 16

18. Canada 17

19. France 17

20. UK 17

21. Russia 18

22. Iceland 19

23. Greenland 20

KU KARANTA: Da duminsa: Mutane 16 sun mutu sanadiyyar wani mummunan hadarin mota a jihar Kano

Ranar Lahadi 5 ga watan Mayu, 2019, aka bayyana cewa an ga watan azumi a fadin duniya, inda aka bukaci kowa ya tashi da azumi jiya Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel