Ganduje zai sauke dukkanin 'yan Majalisar gwamnatin sa, zai nada wadanda ba ya da shakkun biyayyar su a gare sa

Ganduje zai sauke dukkanin 'yan Majalisar gwamnatin sa, zai nada wadanda ba ya da shakkun biyayyar su a gare sa

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a ranar Litinin 6 ga watan Mayu, ya bayyana shirin sa na sauke dukkanin 'yan majalisar gwamnatin sa da manufa ta maye gurbin su da mafiya cancantar rike madafan iko a jihar.

Cikin wani sako da kakakin fadar gwamnatin jihar Kano ya bayyana, Ameen Yassar ya ce gwamna Ganduje ya kudiri wannan aniya da babbar manufa ta inganta ci gaban jihar daidai da kudiri na akidar mataki na gaba wato Next Level.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje
Asali: Twitter

Gwamna Ganduje bayan fatattakar 'yan majalisar gwamnatin sa, ya sha alwashin maye gurbin su da wadanda ba ya da shakku gami da samun cikakken yakini a kan biyayyar su a gare shi.

Kamar yadda kakakin fadar gwamnatin ya bayyana, garambawul a majalisar gwamna Ganduje zai shafi dukkanin masu rike da nadin mukamai da suka hadar da kwamishinoni, hadimai, shugabannin ma'aikatu da makamantan su.

KARANTA KUMA: Kotu ta aikewa da Buhari sammaci a kan tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Onnoghen

A yayin da yiwa majalisar wada-wada ba zai shafi kujerar mataimakin gwamnan jihar Kano ba Nasiru Yusuf Gawuna, gwamna Ganduje ya sha alwashin yiwa hukumar Hizbah garambawul da kuma kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano ta bayyana wannan sanarwa yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da ta gudanar cikin fadar gwamnatin a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel