Ka yi mun gani: El-Rufai ya bayyana yadda za’a karya siyasar uban gida a jahar Legas

Ka yi mun gani: El-Rufai ya bayyana yadda za’a karya siyasar uban gida a jahar Legas

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa karya lagon iyayen gidan siyasan jahar Legas abu ne mai yiwuwa cikin ruwan sauki idan har yan siyasan jahar Legas sun yi abinda ya kamata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito El-Rufai ya bayyana haka ne a garin Ikoyi na jahar Legas, yayin da yake jawabi a yayin taron wasu yan kungiyar ‘Bridge Club’ mai taken ‘Tattaunawar yamma da mai girma gwamnan jahar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai’.

KU KARANTA: Muhimman fa’idojin watan Ramadan guda 11 daya kamata Musulmi ya sani

Kayi mun gani: El-Rufai ya bayyana yadda za’a karya siyasar uban gida a jahar Legas
El-Rufai
Asali: UGC

A jawabinsa, El-Rufai ya bayyana yadda shi da kansa ya gurgunta wasu mutane hudu da ake ganin sune iyayen siyasar jahar Kaduna, don haka yace tsaf za’a iya maimaita kwatankwacin wannan a jahar Legas.

El-rufai ya shawarci mambobin kungiyar da kada su kauce daga shiga siyasa don kawai suna ganin su yan kasuwa ne, inda yace rashin shigarsu siyasa zai lalata musu kasuwancinsu, don haka a cewarsa shigarsu siyasa tafi muhimmanci akan neman kudi.

“A da, Kaduna ta tsinci kanta a irin wannan siyasa ta ubangida, akwai wasu mutane guda uku ko hudu a Kaduna wanda baka isa ka zama wani abu ba sai kana da goyon bayansu, wadannan sune iyayen siyasar jahar Kaduna, kuma dole ka tafi dasu, kana basu kudi a duk lokacin da suka bukata.

“Amma sai muka canza wasan, kuma zuwa bayan zaben 2019 mun yi musu ritaya duka, dole ne muyi, wani daga cikinsu ma cewa yake yi ai shine silar zamana gwamna, kuma sai ya karya ni, kuma a yanzu mun karyashi.” Kamar yadda ya amsa tambayar da tsohon kwamishinan jahar Legas Muiz Banire ya jefa masa.

El-rufai bai tsaya nan ba har sai daya basu dabarun karya iyayen gidan siyasa, inda yace “Kuna da masu kada kuri’u miliyan 6 a Legas, amma miliyan daya ne kacal suka yi zabe a 2019, miliyan 5 basu yi zabe ba, idan har ina da muradin takarar gwamnan Legas, daga yanzu zan fara.

“Zan kaddamar da kwamitin bincike na kwararru don gano dalilin da yasa masu zabe miliyan 5 suka ki fitowa yin zabe a ranar zabe, ina kuma suke zuwa a ranar zaben? Daga nan sai na fara kai musu ziyara a cikin shekaru hudun nan.

“Fatana na samu mutane miliyan biyu kacal daga cikinsu su fito su zabeni, daga nan na ci zabe na gama, kuma zan karya duk wani uban gidan siyasa a Legas, babban abin shine ka samu jama’a, amma fa akwai wahala, yana bukatar aiki tukuru na shekaru uku zuwa hudu."

Daga karshe Gwamna El-Rufai ya shawarci duk mai son tsayawa takarar gwamnan Legas a 2023, ya fara wannan aiki tun daga yanzu, kuma yaana bukatar akalla naira biliyan biyu don gudanar da wannan gagarumin aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel