Wasu Jihohi da aka ga Watan Ramadan a Ranar Lahadi da dare
A yau ne dai aka soma azumin Watan Ramadan a Najeriya da wurare da dama a fadin Duniya. Hakan na zuwa ne bayan da aka samu ganin jinjirin Watan Ramadan a wasu Garuruwan cikin Najeriya.
Mun kawo jerin Garuruwan da aka yi dace da yin ido da jinjirin wannan Wata mai alfarama a jiya. Labarai24 ta bi Kadin labarin inda ta lissafo wasu manyan Garuruwa da aka ga wannan Wata a Ranar Lahadi da karshen yammaci.
Daga cikin wuraren da aka ga Watan na Ramadan akwai; Garin Minna watau babban Birnin Jihar Neja da ke yankin Arewa maso tsakiyar kasar. Haka kuma an samu ganin wannan Wata a cikin babban Birnin Dutse na jihar Jigawa.
KU KARANTA: Ramadan: An ga Watan Azumi a Najeriya inji Sultan
Kamar yadda Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Abubakar Sa’ad III ya bayyanawa Duniya a jiya 6 ga Watan Mayu, da dare, an ga Watan azumin har a Garin Tsafe da ke cikin jihar Zamfara a Ranar karshe na Watan Sha’aban.
Mai alfarma Sultan Abubakar Sa’ad III ya umarci jama’a da su tashi da azumi ranar Litinin, inda ya kuma yi kira ga jama’a su tsaya tsayin-daka da ibada a cikin Watan na Ramadan mai tarin albarka. Musulman Duniya za su yi wata guda su na azumi.
A jiya kun ji cewa Sultan na Sokoto, ya yi kira da a fara gudanar da sallolin tarawihi a cikin dare tuni domin samun tabarraki watan azumi ganin cewa sallar sunna ce mai karfin gaske a addini.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng