2019: Ba da son ran Hukumar INEC aka dage zaben bana ba inji CTA

2019: Ba da son ran Hukumar INEC aka dage zaben bana ba inji CTA

Wata kungiya ta bayyana dalilin dage zaben shugaban kasa a zaben da ya gabata. Kungiyar ta Centre for Transparency Advocacy tace ‘yan siyasan kasar ne su ka shiryawa hukumar zabe makarkasiya.

Centre for Transparency Advocacy take cewa ‘yan siyasa sun shiga cikin hukumar zabe inda su ka shirya mata zagon-kasa, wanda wannan ya sa aka tursasawa hukumar ta INEC ta dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Kungiyar tayi wannan bayani ne a lokacin da ta ke gabatar da wata takarda a game da hakar zabe. A wannan takarda mai tsawon shafi 24, kungiyar ta daura laifin dage zaben ka-co-kam a kan wadannan manyan ‘yan siyasan kasar.

KU KARANTA: INEC tayi wa PDP raddi mai tsauri na cewa an yi wa Atiku magudi

2019: Ba da son ran Hukumar INEC aka dage zaben bana ba inji CTA

An ce dole ta sa INEC ta dage zaben Shugaban kasa da ‘Yan Majalisar Tarayya kwanaki
Source: Original

Jawabin kungiyar ya nuna cewa ‘yan siyasa sun yi amfani da Ma’aikatan wucin-gadi da hukumar INEC ta dauki haya domin a kawowa harkar zaben cikas. Kungiyar tace matsalar aka samu a watan Fabrairu ya fi karfin ita kan-ta INEC.

Kungiyar Centre for Transparency Advocacy tace INEC ba ta da iko a kan jami’an tsaro da kuma babban bankin Najeriya, da kungiyoyin Direbobi na NURTW da su ke taimakawa wajen jigilar kayan zabe don haka tace INEC ba ta da laifi.

CTA tace INEC ta dage zaben ne ba da don ta na so ba, sai dai ganin cewa idan aka yi zabe a lokacin da aka shirya da farko, za a samu magudi na inna-naha. Kungiyar nan tayi wannan jawabi ne Ranar 29 ga Watan nan a cikin Garin Abuja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel