Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun yiwa kauyen Gobirawa kawanya a Katsina

Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun yiwa kauyen Gobirawa kawanya a Katsina

Rahoton da muka samu da Daily Trust ya ce 'yan bindiga sun can suna shirin kai farmaki a kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Safana na jihar Katsina.

'Yan bindigan da adadin su ya kai 200 sun taho a kan babura inda suka yiwa kauyen kawanya suna rera wakokin yaki a cewar wasu mazauna kauyen.

Wata majiya ta shaidawa wakilin Daily Trust cewa 'yan kauyen da wasu 'yan kungiyar sa kai sun fara shirin ko ta kwana idan 'yan bindigan sun kai mus hari.

Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun yiwa kauyen Gobirawa da ke Katsina kawanya

Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun yiwa kauyen Gobirawa da ke Katsina kawanya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Majiyar ta cigaba da cewa ana tsamanin samun dauki daga kauyukan da ke makwabtaka da Gobirawa da kuma jami'an tsaro inda ya ce an sanar da shugabanin karamar hukumar abinda ke faruwa.

Ku biyo domin karin bayani...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel