Masarautar Katsina ta nada sabon hakimin Malumfashi, galadiman Katsina

Masarautar Katsina ta nada sabon hakimin Malumfashi, galadiman Katsina

Masarautar jihar Katsina ta sanar da nadin Sadiq Mahuta a matsayin sabon galadiman Katsina, hakimin Malumfashi.

Sanarwar na kunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga fito daga masarautar Katsina a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu, 2019.

A cikin sanarwar, masarautar ta tabbatar wa Sadiq Mahuta, tsohon alkalin alkalai na jihar Katsina, nadinsa a matsayin sabon galadiman Katsina kuma hakimin Malumfashi.

Nadin Sadiq Mahuta ya biyo bayan mutuwar marigayi mai Shari'a Mamman Nasir, wanda ya rasu a cikin wannan wata da muke ciki.

Masarautar Katsina ta nada sabon hakimin Malumfashi, galadiman Katsina

Sadiq Mahuta

Masarautar Katsina ta nada sabon hakimin Malumfashi, galadiman Katsina

Takardar nadin sabon hakimin Malumfashi, galadiman Katsina
Source: Facebook

A cikin takardar sanarwar da aka rabawa manema labarai, wadda magatakardan masarautar Katsina kuma sallaman masarautar, Alhaji Bello Mamman Ifo, ya sanya wa hannu.

DUBA WANNAN: Dogara ya bukaci a kama shugaban hukumar RMAFC

Da yake tabbatar da nadin, Ifo ya ce mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir, ya amince da nadin Sadiq Mahuta a matsayin Sabon Galadiman Katsina daga ranar Litinin, 30 ga watan Afrilu, 2019.

Yanzu Sadiq Mahuta ya zama daya daga cikin hakimai masu karaga (wadanda keda hannu a nada Sabon Sarki).

Za a Saka ranar da za a yi bikin nadin sarautar nan gaba kadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel