Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Al'umma sunyi matukar murna da farin ciki a ranar Talata bayan an sako matashiya Zainab Habib Aliyu da mahukuntar kasar Saudiyya suka tsare a kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Mataimakin shugaban kasa na musamman kan sabuwar kafar watsa labarai, Bashir Ahmad ne ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta karbo ta daga hannun mahukuntan kasar Saudiyya.

Ma'abota shafukan sada zumunta da sauran al'umma sun bayyana jin dadinsu a kan cigabar da aka samu na sakin matashiyar bayan bincike ya nuna cewa jakar da aka samu dauke da miyagun kwayoyin ba mallakin ta bane.

DUBA WANNAN: Kasar Amurka ta gargadi 'yan kasarta a kan zuwa Najeriya

Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu
Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu
Asali: UGC

Hakan yasa muka gani ya dace mu kawo muku wasu muhimman abubuwa biyar a kan Zainab Aliyu da aka sako.

1. Zainab Aliyu daliba ce a Jami'ar Maitama Sule da ke Jihar Kano

2. Matashiyar tana da shekaru 22 ne a duniya

3. An kama ta ne bayan an gano haramtaciyyar kwayar maganin Tramadol cikin jakar ta, sai dai ta ce wasu ne suka saka kwayar a cikin jakar na ta.

4. Zainab Aliyu da yar uwarta Hajara Aliyu da mahaifiyarsu Maryam Aliyu sun tashi ne daga filin tashi da saukan jirage na Aminu Kano zuwa Saudiyya inda aka tsare ta bayan an gano kwayoyi a cikin wata jaka dauke da sunan ta.

5. An kama ta ne tun a watan Disambar 2018.

A baya-bayan nan ne mahukunta kasar Saudiyyar suka yanke hukuncin kisa ga wata 'yar Najeriya da aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164