‘Yan Sanda sun kama Saurayi ya saci Madubin Likita a Malumfashi

‘Yan Sanda sun kama Saurayi ya saci Madubin Likita a Malumfashi

Jami’an ‘Yan Sandan jihar Katsina sun damke wani Mutumi mai suna Hamza Sani da ake zargin da hada kai da wasu mutum 4 wajen sace wasu kayan aiki a babban asibitin da ke cikin Garin Malumfashi.

Kamar yadda mu ka samu labari dazu, wannan mutumi mai shekaru 30 a Duniya ya shiga hannun Jami’an tsaro ne bisa zargin sa da ake yi da sace na’urar da ake amfani da ita wajen hango kwayoyin halitta da cututtuka a asibiti.

Damke Hamza Sani da aka yi, ya taimakawa Jami’an tsaro wajen cafke wasu wanda ake zargi da yin sata a wannan babban asibitin gwamnatin Jihar Katsina da ke Malumfashi. Hamza shi ne ya tona asirin wadannan Abokan aikin na sa.

Wadanda ‘Yan Sandan su ka damke ta hannun Hamza su ne: Magaji Yusuf, 36; Saidu Shehu, 40; Kamala Aliyu, 33; da kuma Emmanuel Ukelere, 48. Ana zargin wadannan mutane da shiga asibitin da yin sata ba sau daya ba, ba sau biyu ba.

KU KARANTA: Alkali yayi nisan kiwo wajen fara shari'ar Bala Mohammed a Kotu

‘Yan Sanda sun kama Saurayi ya saci Madubin Likita a Malumfashi

‘Yan Sanda sun cafke wasu hatsabiban Barayin asibiti

Kakakin ‘Yan Sanda na Yankin, Gambo Isa, ya bayyanawa manema labarai wannan inda yace Hamzah da mutanensa, sun saba zuwa asibiti su sace kaya domin su saida. Hamza Sani ya kuma amsa laifinsa, ya kuma tona asirin sauran mutanen.

Daga cikin kayan da Hamza Sani ya sace akwai na’urar nan ta ‘Microscope’ watau Madubin Likita wanda ake saidawa a kan kudi Naira miliyan 1.7. Hamza yace ya saida wannan na’ura ne a N5, 000 domin ya samun kudin kai Matarsa asibiti.

Dubun wannan mutumi da sauran ‘yan uwan aikin na sa ta cika ne bayan da ya shiga babban asibitin Garin Malumfashi da ke cikin jihar Katsina inda aka same shi da kayan asabiti iri-iri a hannunsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel