Rikicin Gombe: Shugaba Buhari ya nuna matukar alhini da takaici

Rikicin Gombe: Shugaba Buhari ya nuna matukar alhini da takaici

Labari ya zo mana a cikin jiya cewa shugaba Muhammadu Buhari ya aiko ta’aziyyarsa ta musamman a game da wasu Bayin Allah; maza da kuma ‘yan mata da aka kashe a cikin Garin Gombe kwanaki.

Idan ba ku manta ba, a jiya Asabar 27 ga Watan Afrilu rikici ya nemi ya barke a jihar Gombe, yayin da ake kokarin yin jana’izar wasu mutum 9 da aka kashe a lokacin bikin Easter da aka yi a makonnin da su ka shude a fadin Duniya..

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda yanzu yana Birnin Landan a kasar Ingila, ya fito yayi magana a game da wannan rashi da aka yi, shugaban kasar ta bakin Hadiminsa yace sam bai ji dadin wannan abin takaici da ya auku ba.

Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. A jawabin na Garba Shehu, shugaban kasar ya nuna jimaminsa inda yace daukacin al’ummar kasar su na makokin wannan abu da ya faru.

KU KARANTA: Ya kashe Matar Maigidansa saboda an kore sa daga aiki

Rikicin Gombe: Shugaba Buhari ya nuna matukar alhini da takaici
Gwamnatin jihar Gombe ta hana yawo a Gari bayan rikici ya barke
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya kuma yi addu’a ga wadanda wannan rashi ya auku a gare su, da Ubangiji ya ba su karfin juriya da hakuri a wannan lokaci na takaici. Kusan wannan ne jawabin shugaban kasar na farko bayan barin sa Najeriya.

A jiya an samu takaddama wajen bizne wadannan mutane da aka kashe bayan da masu jana’izar su ka rufe hanyoyin cikin Garin Gombe, wannan ya jawo jama’a su buda hanyoyin da karfin tsiya, har kuma lamarin ya kai ga rikici.

Buhari ya nuna matukar mamakin da jin labarin cewa har ta kai an sa takunkumin fita a Birnin Gombe bayan abin da ya auku jiya. Shugaban kasar ya nemi jami’an tsaro su tashi tsaye wajen ganin an wanzar da zaman lafiya a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel