Jami'ar Skyline tayi bikin daukan sabbin dalibai a karo na farko a Kano (Hotuna)
Skyline University Nigeria (SUN), jami'a mai zaman kanta ta farko a jihar Kano, tayi bikin daukan sabbin dalibai 82 a karo na farko da zasu fara karatun digiri a zangon shekarar 2018/2019.
An dauki daliban ne a tsangayoyin karatu daban-daban da jami'ar keda su, wadanda suka hada da 'Arts Management & Social Sciences (SAMSS) da 'Science & information Technology (SSIT).
Jami'ar ta fara bayar da gurbin karatun digiri ga dalibai ne bayan samun sahalewar hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC).
Da yake gabatar da jawabi a wurin taron bikin karbar daliban, shugaban jamai'ar, Farfesa Sudhakar Kota, ya shawarci sabbin daliban da su yi amfani da damar samun gurbin karatu a jami'ar wajen samun ilimin da zai basu damar taimakon al'umma da kasa baki daya.
Kota ya ce makarantar ta samu gagarumar nasara da ta samu damar fara daukan dalibai a zangon karatu na 2018/2019.
Kazalika ya yi kira ga daliban da su yi amfani da kayan aiki na zamani masu inganci da jami'ar keda su wajen samun ilimi mai nagarta da zai basu damar a goga da su a ko ina cikin duniya.
DUBA WANNAN: Rundunar soji ta tabbatar da kashe 'yan bindiga 4 a Zamfara
Shugaban ya bayyana cewar jami'ar, zata samar da karin wasu tsangayoyin karatu a bangaren ilimin shari'a da ilimin harkokin lafiya da Najeriya da duniya ke nema.
A karshe, rijistaran jami'ar, Mista Satya Vir Sighn, ya rantsar da sabbin daliban da aka dauka, sannan sun 'sa hannu' a sabuwar rijistar makaranta domin tabbatar dasu a matsayin halastattun daliban jami'ar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng