Zababben gwamnan Borno ya dauki alkawarin cigaba da ayyukan alherin Kashim

Zababben gwamnan Borno ya dauki alkawarin cigaba da ayyukan alherin Kashim

Zababben gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa a matsayinsa na gwamna mai jin gado, zai tabbatar da cigaba da ayyukan alherin da maigidansa, Gwamna Kashim Shettima ya fara.

Zulum ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook inda yayi alkawarin daurawa daga inda Gwamna Kashim Shettima ya tsaya, musamman duba da dimbin ayyukan more rayuwa daya dauko.

Zababben gwamnan Borno ya dauki alkawarin cigaba da ayyukan alherin Kashim
Makaranta a Borno
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana muhimmiyar hanyar yaki da ta’addanci a Najeriya

Haka zalika Farfesan ya kara da cewa game da sababbi, manya kuma kayatattun makarantun da gwamnan jahar Borno ya gina kuwa, zai tabbata ya dauki sabbin nagartattun Malamai da zasu koyar a wadannan makarantu don ilimantar da dalibai.

Zababben gwamnan Borno ya dauki alkawarin cigaba da ayyukan alherin Kashim
Buhari da Kashim
Asali: Facebook

Daga karshe zababben gwamna Babagana Umara Zulum ya bada tabbacin zai tabbatar da bin doka da ka’ida a wajen tafiyar da mulki a gwamnatinsa, ba tare da cin amanar da jama’a suka bashi ba.

A wani labarin kuma shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana babbar hanya mafi inganci wajen yaki da ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, inda yace samar da ingantaccen ilimi shine kadai hanyar kawar da Boko Haram daga ban kasa.

Zababben gwamnan Borno ya dauki alkawarin cigaba da ayyukan alherin Kashim
Buhari da Kashim
Asali: Facebook

Buhari ya bayyana haka ne garin Maiduguri yayin ziyarar kwana daya daya kai jahar Borno a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, inda ya kaddamar da manya manyan ayyukan more rayuwa da gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima ya yi.

“Wannan shine dabarar kawar da ta’addancin Boko Haram, ilimi na taka rawa sosai wajen samar da gogayya tsakanin mutane tare da inganta rayuwarsu.” Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng