Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane

Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane

- An kama wani dalibin jami'a da yunkurin satar wani mutumi mai suna Chinedu Odenigbo

- Sai dai kuma shi dalibin ya ce gaskiyar magana abokinshi ne ya yaudareshi ya ja shi cikin wannan harkar

A jiya Alhamis ne 25 ga watan Afrilu, 2019, rundunar 'yan sandan jihar Neja ta ce ta kama mutane uku da yunkurin sace wani mutumi mai suna Chinedu Odenigbo da ke Angwan Kadara yankin Maitumbi, cikin garin Minna, babban birnin jihar Neja.

An shaidawa hukumar 'yan sanda faruwar lamarin ranar 18 ga watan Afrilu, 2019, wanda wani mutumi mai suna Emenike Odenigbo ya kira hukumar ya ke bayyana mata cewa ya kama wasu mutane biyu suna kokarin sace mishi dan shi mai suna Chinedu.

Wadanda ake zargin, Onwan Onyedika mai shekaru 20 da Eze Athanasius mai shekaru 27 duka daga jihar Enugu, 'yan sandan da ke yankin Maitumbi ne suka kama su.

Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane
Ni dan fashi da makami ne kawai, bana garkuwa da mutane
Asali: Twitter

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin dalibi ne a jami'ar Najeriya, Nsukka, ya shiga harkar sace mutanen ne saboda ya samu ya yi kudi da wuri.

Dalibin mai suna Onyedika, wanda ke aji hudu a jami'a, ya bayyanawa manema labarai cewa abokinshi Sunday ne ya yaudare shi ya shigo da shi cikin wannan badakalar.

Ya ce, "Sunday ya gaya mini cewa zai fara sana'a, kuma ya roke ni da in tafi tare dashi zuwa gidan dan uwanshi dake garin Minna domin muyi mishi fashi, inda ya ce yiwa dan uwan nashi fashi ita ce hanya daya kawai da zasu samu kudin yin sana'ar, sai ni kuma na bishi.

KU KARANTA: Bidiyon Lady Gaga na rera karatun Al-Qur'ani Suratul Al-Duha

"Ban san yadda aka yi na tsinci kai na a cikin wannan matsalar ba. Ban san cewa abokin nawa na da wata manufa a ranshi ba. Gaskiyar magana na biyo shi ne don mu saci kudin 'ya'yanshi ba da niyyar zuwa mu saci danshi ba.

"Na ci amanar mahaifina wanda ya rasu, ba ni da wani dalili na shiga cikin wannan rikicin. Ban san yadda zan kalli mahaifiyata ba. Na ba ta rayuwata gaba daya."

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa za a mika wadanda ake zargin zuwa kotu bayan sun kammala bincike a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel