An yiwa dan kasar China nadin sarauta a jihar Kano

An yiwa dan kasar China nadin sarauta a jihar Kano

Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu ya nada Mike Zhang sarauta a matsayin 'Wakilin 'Yan China a Kano' a fadarsa da ke cikin birnin Kano

Sarkin Kano ya nada wani dan kasar China sarauta.

An nada Mike Zhang a matsayin wakilin 'yan China a Kano.

Wannan shi ne karo na farko da aka fara nada sarautar a birnin Kano.

Ga bayanin da Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya yi a lokacin nadin sarautar: "Mun baka wannan wakilci ne, na wakilin 'yan China a Kano."

'Yan China sun yi shigar gargajiya irin ta kasar Hausa domin su taya Mike murna.

A na shi bayanin da ya yi cikin harshen Hausa Mike Zhang ya ce, "Zan cigaba da bayar da gudummawa don cigaban Najeriya da jihar Kano baki daya."

Zhang shahararren dan kasuwa ne, wanda ya shafe shekaru sama da 17 yana harkar kasuwanci a cikin birnin Kano.

KU KARANTA: Hotuna: Yanzun nan shugaba Buhari ya isa jihar Borno

Rahotanni sun nuna cewa Zhang shine dan kasar China na farko da aka yi wa nadin sarauta a Arewacin Najeriya.

Shi ne ya mallaki babban kamfanin nan na ruwan roba na Maya da ya ke unguwar Sharada.

Sarkin Kanon ya ce ya ba shi sarautar ne saboda irin kokarin da ya ke da shi na habbaka harkar kasuwancin aa jihar Kano, kuma yana fatan nadin sarautar zai kara bashi karfin gwiwar cigaba da gudanar da kasuwanci a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng