Bidiyon Lady Gaga na rera karatun Al-Qur'ani Suratul Al-Duha

Bidiyon Lady Gaga na rera karatun Al-Qur'ani Suratul Al-Duha

Wani faifan bidiyo na yawo a kafar sada zumunta ta yanar gizo da ke nu ni da shahararriyar mawakiyar nan Lady Gaga ta na rera karatun Al-Qur'ani mai girma cikin murya mai dadi, inda ta ke karanta Suratul Al-Duha

An nuna wani faifan bidiyo sama da miliyan daya a yanar gizo, wanda ke nuni da wata mata wacce ake tunanin cewa fitacciyar mawakiyar nan ce ta kasar Amurka, Lady Gaga, ta ke rera karatun Al-Qur'ani mai girma.

Wani mutumi mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook ne ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa ranar 30 ga watan Maris, an bayyana cewa an kalli faifan bidiyon kusan sau 223,000, sannan kuma an yada shi har sau 12,000.

Mutumin ya sanyawa bidiyon suna, "Mawakiyar Kasar Amurka Stefani Joanne Lady Gaga ta shammaci Amurka da Turawa da irin yadda ta ke karanta Suratul Al-Duha."

Hakazalika wani shafin sada zumunta na kasar Pakistan mai suna Pakistan News International ya wallafa bidiyon, inda aka kalle shi sama da sau 690,000.

Bayan haka kuma, mutane musamman 'yan Najeriya sun rika tallata bidiyon a shafukan sada zumunta musamman WhatsApp da Facebook. Sannan kuma an yada bidiyon a shafin Twitter da YouTube ba adadi.

KU KARANTA: Hotuna: Yanzun nan shugaba Buhari ya isa jihar Borno

Shin wace mata ce a bidiyon?

Gaskiyar magana ba Lady Gaga ba ce a cikin bidiyon.

A wani bincike da wani kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi, ya gano cewa matar wata shahararriyar mawakiya ce 'yar kasar Tunisiya, mai suna Sofia Sadek.

Sofia Sadek ta shahara matuka a yankin Arewacin Afirka a fannin waka.

Kamfanin ya gano cewa faifan bidiyon ya samo tushe ne daga shafin yanar gizo na YouTube, inda gidan Rediyon Med ya wallafa shi a ranar 24 ga watan Satumbar shekarar 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel