'Yan siyasa ke da alhakin ta'addancin 'yan baranda da masu garkuwa da mutane - Falana

'Yan siyasa ke da alhakin ta'addancin 'yan baranda da masu garkuwa da mutane - Falana

Zakakurin lauya kuma gogagge a kan fafutikar kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ya zargi 'yan siyasa da kasancewar su a matsayin ummul aba isin duk wani kalubale da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Femi Falana

Femi Falana
Source: Depositphotos

Mista Falana ya ce miyagun ababe da 'yan siyasa suka mallakawa makamai domin cimma manufofin su a lokutan zabe, a halin yanzu su na ci gaba da zartar da ta'addanci na kashe-kashe da zubar jinin al'umma.

Gogaggen Lauyan ya yi furucin haka yayin wani shiri na Sunrise da kafar watsa labarai ta Channels TV ta shirya a ranar Talata. Ya ce masu ta'addancin kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a sassan kasar nan sun kasance miyagun ababe da 'yan siyasa suka mallakawa makamai a lokutan zabe.

KARANTA KUMA: Carles Puyol ya iso Najeriya domin ganawa da masoya gasar kofin zakarun Turai

Cikin kalami nasa, Mista Falana ya ce ci gaba da yaduwar ta'addancin kashe-kashe gami da garkuwa da mutane da su ka addabi al'ummar kasar nan a halin yanzu na da nasaba babban zaben kasa da ya gudana a kwana-kwanan nan.

Kalli Bidiyon:

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel