Carles Puyol ya iso Najeriya domin ganawa da masoya gasar kofin zakarun Turai

Carles Puyol ya iso Najeriya domin ganawa da masoya gasar kofin zakarun Turai

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Carles Puyol, ya iso Najeriya domin wata ziyarar kwanaki uku da ya kawo ta yawon shawagi na ganawa da masoya gasar kofin zakarun turai da ke kasar nan ta Najeriya.

Puyol wanda ya kasance tsohon shugaba mai rike da kambun jagorancin 'yan kwallon kafa na kungiyar Barcelona, zai shafe tsawon kwanaki na yawon shawagi a cikin birnanen Akwa Ibom da kuma Legas domin ganawa da masoya kwallon kafa.

Carles Puyol
Carles Puyol
Asali: UGC

Tsohon dan wasan mai tsaron gida a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ya kafa tarihi na lashe gasar La Liga karo shida yayin da ya lashe gasar kofin zakarun Turai sau uku da kuma sauran kyaututtuka da ya samu a kasar Andalus wato Spain.

Bayan bugawa kasar sa ta Spain manyan wasanni 100 a tarihin kwallon kafa, ya kuma bayar da gagarumar gudunmuwa wajen samu nasarar ta lashe gasar Euro a shekarar 2008 da kuma gasar kofin duniya a shekarar 2010.

KARANTA KUMA: Yadda jarrabawar bana ke kasancewa - JAMB

Yayin dirar sa a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom da safiyar yau ta Talata, Puyol ya yi arangama da dubunnan masoya kwallon kafa da suka yi masa lale maraba. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Puyol zai buga wani wasa tare da tsohon dan wasan Najeriya, Austin Jay Jay Okocha.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kotun Najeriya ta bayar da umurnin cafke tsohon dan wasan Najeriya Jay Jay Okocha sakamakon zargin sa da laifin kauracewa biyan haraji da ya rataya a wuyan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel