Neman abinci ya sanya na shiga ta'addancin garkuwa da satar shanu - 'Dan ta'adda

Neman abinci ya sanya na shiga ta'addancin garkuwa da satar shanu - 'Dan ta'adda

Daya daga cikin miyagun ababe masu ta'addancin garkuwa da mutane da kuma satar shanu da hukumar 'yan sanda jihar Neja ta cafke, ya bayyana nemawa iyalan sa abinci a matsayin dalilin da sanya ya dauki wannan hanya da ba ta bullewa.

Daya daga cikin miyagun 'yan ta'adda biyar da hukumar 'yan sandan jihar Neja ta cafke da laifin garkuwa da wani Mutum, 'ya'yan sa biyu da kuma satar shanu 54, ya ce neman hanyar arziki cikin gaggawa domin sauke nauyin iyalin sa ya sanya ya shiga wannan mummunar harka.

Neman abinci ya sanya na shiga ta'addancin garkuwa da satar shanu - 'Dan ta'adda
Neman abinci ya sanya na shiga ta'addancin garkuwa da satar shanu - 'Dan ta'adda
Asali: UGC

Miyagun ababen Abubakar Rabi'u, Sani Isah, Abubakar Isah, Adamu Yakubu, da kuma Sule Musa, sun shiga hannun jami'an tsaro bayan sun yi garkuwa da wani mutum, Abubakar Umar tare da 'ya'yan sa biyu da kuma shanu 54 a kauyan Bangi dake karamar hukumar Mariga ta jihar Nasarawa.

Daya daga ababen zargin, Sani Isah, ya bayar da shaidar cewa ya afka cikin wannan mummunar harka ta yiwa kasa fasadi domin samun arziki da dukiya cikin gaggawa da zai sauke nauyin iyali da rataya a wuyan sa.

A yayin da dan ta'adda Sani ya shafe tsawon shekaru 15 ya na sana'ar hako ma'adanan kasa, cikin rashin tawakkali ya ce rashin samun wadatar ciyar da iyalan sa abinci sau uku a ko wace rana ya sanya ya afka cikin tarkon shaidan ba tare da wata-wata ba.

KARANTA KUMA: Rayuka 15 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Muhammad Abubakar, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari yayin da dukkanin ababen zargin su ka amsa laifin su inda tuni sun ci kasuwar shanu takwas cikin 54 da suka sata.

Ba ya ga bayar da tabbacin gudanar da bincike domin gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya, babban jami'in dan sandan ya ce hukumar ta samu nasarar ceto sauran shanu 46 da suka rage.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel