Tuna baya: Abubuwan da Sa'adu Zungur ya fada a kan makomar arewa shekaru 61 da suka wuce

Tuna baya: Abubuwan da Sa'adu Zungur ya fada a kan makomar arewa shekaru 61 da suka wuce

A yayin da arewacin Najeriya ke fama da kalubale daban-daban da suka hada da na tsaro, tabarbarewar tarbiyya da lalacewar tattalin arziki, Legit.ng tayi waiwaye domin kawo maku kalaman fasihin mawaki, Marigayi Sa'adu Zungur, a cikin daya daga cikin waken sa mai taken: 'Arewa Jamhuriyya Ko Mulukiyya? ".

Sa’adu Zungur (1914-- 1958): Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya?

 • “Matukar a arewa da karuwai,

‘Yan daudu da su da Magajiya.

 • Da samari masu ruwan kudi,

Ga mashaya can a gidan giya.

 • Matukar ’ya’yan mu suna bara,

Titi da Loko-lokon Nijeriya.

 • Hanyar birni da na kauyuka,

Allah baku mu samu abin miya.

 • Sun yafu da fatar bunsuru,

Babu mai taryonsu da dukiya.

 • Babu shakka’ yan kudu za su hau,

Dokin mulkin Nijeriya.

Tuna baya: Abubuwan da Sa'adu Zungur ya fada a kan makomar arewa shekaru 61 da suka wuce

Marigayi Sa'adu Zungur
Source: Facebook

 • In ko ’yan kudu sunka hau,

Babu sauran dadi, dada kowa zai

sha wuya.

 • A Arewa zumunta ta mutu,

Sai karya sai sharholiya.

 • Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen,

Malaman karya ’yan damfara.

 • Sai karya sai kwambon tsiya,

Sai hula mai annakiya.

 • Ga gorin asali da na dukiya,

Sai kace dan annabi fariya.

DUBA WANNAN: Abun kunya: An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso

 • Jahilci ya ci lakar mu duk,

Ya sa mana sarka har wuya.

 • Ya sa mana ankwa hannuwa,

Ya daure kafarmu da tsarkiya.

 • Bakunan mu ya sa takunkumi,

Ba zalaka sai sharholiya.

 • Wagga al’umma mai za ta yo,

A cikin zarafofin duniya.

 • Kai Bahaushe ba shi da zuciya,

Za ya sha kunya nan duniya.

 • “Mu dai hakkin mu gaya muku,

Ko ku karba ko ku yi dariya.

 • Dariyar ku ta zam kuka gaba,

da nadamar mai kin gaskiya.

 • Gaskiya ba ta neman ado,

Ko na zakin muryar zabiya.

 • Karya ce mai launi bakwai,

Ga fari da baki ga rawaya.

 • Ga kore ga kuma algashi,

toka-toka da ja sun garwaya”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel