Mutane uku sun haifi da daya a lokaci daya

Mutane uku sun haifi da daya a lokaci daya

Wasu kwararrun likitoci a bangaren haihuwa a kasar Sipaniya da Girka sun bayyana yadda su ka samo wani jariri ta hanyar kimiyya, inda suka yi amfani da kwayayen haihuwa na mutane uku, don su kawo karshen matsalar haihuwar wata mata.

An haifi yaron ranar Talatar nan wanda ya ke da nauyin kilo 2.9, sannan an bayyana cewa mahaifiyar da yaron suna cikin koshin lafiya.

Mutane uku sun haifi da daya a lokaci daya

Mutane uku sun haifi da daya a lokaci daya
Source: Depositphotos

Likitocin sun bayyana cewa suna gabatar da wani tsari a bangaren likitanci, wanda ba a taba yin irin shi ba, tsarin wanda suka bayyana cewa zai taimakawa ma'aurata wadanda su ke fama da matsalar rashin haihuwa.

Wasu masana a kasar Birtaniya sun ce shirin ya kawo kace-nace a cikin al'umma, wanda da yawa suke ganin bai kamata ace an gudanar da shirin ba.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Tsarin gwajin haihuwar an gudanar da shi ta hanyar amfani da kwan haihuwar uwar, da ruwan maniyin uban da kuma na wata mata da ta bada kwan haihuwarta don taimako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel