Shugabancin majalisa: Lawan ya bijrewa umurnin Oshiomhole, ya nemi goyon bayan 'yan PDP

Shugabancin majalisa: Lawan ya bijrewa umurnin Oshiomhole, ya nemi goyon bayan 'yan PDP

Jagoran majalisa kuma dan takarar kujerar shugabancin majalisar dattaawa na majalisa ta tara a jam'iyyar APC, Sanata Ahmad Lawan ya gana da wasu gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a yunkurinsa na ganin ya samu hadin kansu wurin lashe zaben shugabancin majalisar.

Sai dai wannan ya sabawa matsayar shugabanin jam'iyyar ta APC inda a baya suka ce ba bu bukatar da suka kai da jam'iyyar PDP domin zaben shugaban majalisa da suke so.

Zaben Lawan da Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ta yi ya janyo rabuwar kai a jam'iyyar inda Sanat Ali Ndume na jihar Borno da Danjuma Goje na jihar Gombe suka tubure cewar suma sai sun shiga sahun masu takarar kujerar majalisar.

Jim kadan bayan kwamitin zartarwa na jam'iyyar ta APC ta zabi Lawan, shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole ya ce ba su bukatar 'yan majalisun jam'iyyar APC domin samun nasarar lashe zaben kujeru a majalisar na tarayya.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Shugabancin majalisa: Lawan ya bijrewa umurnin Oshiomhole, ya gana da gwamnonin PDP

Shugabancin majalisa: Lawan ya bijrewa umurnin Oshiomhole, ya gana da gwamnonin PDP
Source: UGC

Ya yi gargadin cewa kada a sake ayi wata yarjejeniya na yin mulki tare da jam'iyyar ta adawa.

APC ta ce sanatocin ta ne za su jagoranci dukkan kwamitocin majalisar na tarayya.

Sai dai Lawan ya gana da gwamnonin jam'iyyar PDP guda uku a cikin makon nan domin neman goyon bayan su.

Punch ta ruwaito cewa ya gana da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da zababen Gwamnan jihar Imo, Emeke Ihedioha a Abuja inda ya nemi goyon bayansu a takarar da ya ke yi na shugabancin majalisa.

Wani majiya a daga taron da akayi da Tambuwal a ranar Laraba ya ce Lawan ya koka game da kalamen da Oshiomhole ya fadi game da PDP inda ya ce hakan ya kawo masa cikas wurin samun goyon bayan wasu sanatocin PDP.

Sai dai ba a bayyana matsayar Lawan a kan batun yin mulki tare da PDP ba.

"Kawai dai ya gana da su ne domin ya tabbatar musu niyyarsa na yin aiki tare da su," inji majiyar.

Kakakin kungiyar yakin neman zaben Lawan, Sanata Sabi Abdullahi ya tabbatarwa majiyar Legit.ng cewa Lawan ya gana da wasu gwamnoni amma bai fadi sunayen gwamnonin ba ko abinda suka tattauna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel