Dan acaba ya kashe fasinja akan naira dari biyu
- Wata kotu ta aika wani dan acaba gidan kaso, bayan ta kama shi da laifin amfani da adda ya sara fasinjansa, akan kudin acaba naira 200
- Lamarin ya faru ne a garin Ilorin babban birnin jihar Kwara a yau Juma'ar nan
A ranar Juma'ar nan ne kotun majistare dake Ilorin babban birnin jihar Kwara, ta tura wani dan acaba mai suna Umar Kareya, gidan kurkuku, bayan ta kama shi da laifin kashe fasinjansa akan kudin acaba naira 200.
Alkalin kotun, Mai Shari'a Jumoke Bello, wacce ta ki yarda da uzurin da wanda ake tuhumar ya kawo, saboda rashin kwararan hujja, ta umarci a tsare shi a gidan kurkukun Oke-Kura da ke cikin garin Ilorin.
Alkalin ta daga sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Afrilu.
Wacce ta gabatar da wanda ake tuhumar, Sgt. Roda Kayode, ta shaidawa kotu cewa wanda ake tuhumar ya dauki marigayin wanda ba a bayyana sunanshi ba, daga unguwar Labe-Labe zuwa kasuwar Fumuni ta hanyar Bani a karamar hukumar Baruteen dake jihar ta Kwara.
Kayode ta ce, akan hanyarsu ne rikici ya balle a tsakaninsu, akan kudin acaba.
KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya
Suna cikin wannan rikici ne, sai wanda ake tuhumar ya yi amfani da adda, ya sari marigayin, inda ya yi mishi mummunan rauni da ya yi sanadiyyar rasa rayuwarsa.
Ta ce, an kama wanda ake tuhumar a wurin da lamarin ya faru, bayan mutane sun hankalta da abinda ke faruwa.
Ta roki kotu ta tsare wanda ake tuhumar har sai an kammala bincike akan shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng