Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

A cikin 'yan kwanakin nan ne aka rika yada wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda jaruman Kannywood Hadiza Gabon ta rika shararawa jaruma Amina Amal mari tare da tsangwaman ta a daki tana mata tambaya a kan wani tes da ta aika mata.

A cikin bidiyon, an rika jin muryar da akayi ikirarin na Gabon tana cewa a bari ta yiwa Amal dukan tsiya saboda wai tayi mata sharri yayin da ita kuma Amal tayi zugum zaune a kan gado tana sauroron Gabon tana ba ta hakuri.

Amal din ta rika fada wa Gabon cewa ta yafe mata domin kuskure ne inda hasali ma ta ce ita ba ta san lokacin da ta aika wannan sakon ba a yayin da ta ke tilasta mata ta karanta sakon.

Zargin Madigo: Hadiza Gabon ta fitsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari
Zargin Madigo: Hadiza Gabon ta fitsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Wani da ke tare da Gabon a wurin ya yi kokarin hana ta cigaba da dukan Amal amma hakan ya ci tura inda daga bisani shine ya karanta sakon.

"Salam, Yar uwa ta, don Allah idan ba kya komai anjima ina son ganin ki, ma'assalam." kamar wani aka karanto sakon.

Al'umma sun rika bayyana mabanbanta ra'ayoyinsu a kan lamarin inda wasu suka ce abinda Gabon ta aikata zalunci ne da fin karfi wasu kuma suka rika yi mata uzuri da cewa bacin rai ne ya janyo haka kuma hakan zai iya faruwa da ko wanne dan adam.

Hakan ya sa suka bukaci al'umma su dena ruruta wutan gaba tsakanin jaruman kuma abinda ya fi dacewa shine ayi kokarin sulhu tsakanin su.

An dade dai ana zargin wasu 'yan Kannywood da madigo a tsakaninsu inda a shekarun baya wasu jarumai kamar Adam Zango da Mustapha Naburaska suka fito fili suka soki abin inda suka ce ba su cikin masu aikata wannan lamarin.

Ga bidiyon nan a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164