‘Yan ta’adda sun karbe wasu bangarorin Jihar Katsina – Masari
Wasu bangorori na jihar Katsina su na hannun miyagu kamar yadda gwamnan jihar, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana. Gwamnan ya bayyanawa sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, wannan a makon nan.
Mataimakin gwamnan jihar Katsina watau Alhaji Mannir Yakubu, shi ne ya wakilci gwamna Aminu Masari a lokacin da ya gana da shugaban ‘yan sandan Najeriya IGP Muhammed Adamu, a Ranar Laraba 10 ga Watan Afrilu na 2019.
Wakilin gwamnan yake cewa wadannan Miyagu sun karbe wasu yanki a Katsina inda su ke cin karen su babu babbaka. Alhaji Mannir Yakubu yake fadawa Sufetan ‘yan sanda cewa wadannan Miyagu su na kashe jama’a babu kaukutawa.
KU KARANTA: An sake kai wani mummunan hari a cikin Jihar Katsina
Yakubu ya kara da cewa Sufetan ‘Yan Sanda Adamu ya zo jihar a daidai lokacin da ya dace. Mataimakin gwamnan ya kara jadadda cewa irin su karamar hukumar Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa da kuma Faskari su na fama da rashin tsaro.
Haka zalika wadannan Miyagu da ke satar jama’a sun yaiyabe yankin Sabuwa, Dandume da karamar hukumar Kankara. Kwanakin baya dai Shugaban ‘yan sandan kasar ya kawo ziyara zuwa jihar inda yayi alkawarin inganta harkar tsaro.
Yakubu yace wadannan wurare da ake satar mutane su na kan iyaka ne da jihar Zamfara inda rikici yayi kamari. Mataimakin gwamnan na Katsina ya fadawa IGP Adamu akwai bukatar ‘yan sanda sun gano masu aikata wannan mugun laifi.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng