Kalli wasu yan fashi da makami da aka kama sanye da kayan jami’an Yansanda

Kalli wasu yan fashi da makami da aka kama sanye da kayan jami’an Yansanda

Rundunar Yansandan jahar Neja ta sanar da kama wasu miyagun yan fashi da makami guda biyu dake sanye da kayan Yansanda, suna basaja a matsayin Yansanda suna kwatar kayana jama’a a jahar Neja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dubun yan fashin ta cika ne a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu yayin da suke aikata aika aikansu a unguwar Liman Madalla, cikin karamar hukumar Suleja na jahar Neja.

KU KARANTA: Babu gagararre sai bararre: Yadda mayakan Sojan sama suka halaka yan bindiga

Kalli wasu yan fashi da makami da aka kama sanye da kayan jami’an Yansanda

Kalli wasu yan fashi da makami da aka kama sanye da kayan jami’an Yansanda
Source: UGC

Rundunar ta bayyana sunayen yan fashin kamar haka; Shu’aibu Pawa mai shekaru 27, da Masa’udu Haruna mai shekaru 25, inda tace ta samu nasarar kamasu ne a garin Madalla bayan samun bayanan sirri game da danyen aikin da suke aikatawa.

Bugu da kari bincike ya nuna yan fashin sun samu kayan Yansandan ne bayan sun shiga gidan wani jami’in Dansanda mai suna Abdullahi Abubakar inda suka kwashe masa kayan aiki da sauran kayayyakinsa.

Guda daga cikinsu, Haruna Masa’udu ya bayyana cewa suna aikata fashi da makami a duk lokacin da suka ga dama sakamakon suna sanye da kayan sarki.

“Muna sanya karafa akan hanya don fasa tayoyin motocin matafiya, da zarar sun tsaya sai muyi musu fashi, kuma muna yin wannan aiki ne don kulawa da kanmu.” Inji shi.

Sai dai Haruna ya bayyana cewa basu da bindiga, don kuwa bindigar roba suke amfani dashi, amma suna amfani da muggan makamai kamarsu wukake, adduna da sauran samfurin miyagun makamai wajen kai ma jama’a hari.

Da yake nasa jawabin, kaakakin rundunar Yansandan jahar Neja, Muhammad Abubakar ya bayyana cewa yan fashin sun amsa laifinsu, kuma sun kwato bindigu guda biyu daga wajensu, wukake biyu da kayanYansanda, sa’annan yace zasu mikasu gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel