Hanyar lafiya: Abubuwa 10 da ya kamata ku kiyaye lokacin zafi
- Juyawar duniya kan kawo canjin yanayi daga damuna zuwa hunturu zuwa yanayin zafi
- Yanayin zafi na galabaitar da mutane, dabbobi, tsuntsaye, kwari da sauran ragowar halittu da ke rayuwa a doron kasa da ma karkashinta
- Ana samun barkewar cututtuka da annoba da dama a yanayin zafi
A yayin da duniya ke juyawa sau daya a cikin kowacce shekara, ana samun canjin yanayi daga damuna zuwa hunturu (sanyi) zuwa yanayi na zafi.
A lokacin zafi, ana samun budewar rana, lamarin da ke kara dumama yanayin jiki da na muhalli. Irin wannan dumamar yanayi da zafi ke zuwa da ita, na saka mutane da dabbobi da tsuntsaye, har ma da kwari su takura, wanda hakan ke saka su neman inuwa domin samun sa'ida.
Son fake wa a inuwa domin samun sauki daga zafin rana da dumamar yanayi, bai tsaya iya ga mutane ba kadai, hatta dabbobi da kwari kan nemi inuwa domin su fake. Sai dai, a irin wannan lokaci, wasu dabbobi masu hadari da dafi kan cutar da mutane a kokarinsu na son ganin mutum bai hana su more wa ba.
Yanayi na zafi kan zo da cututtuka da dama, baya ga samun barkewar annoba da daban-daban.
Ga jerin wasu abubuwa 10 da ya kamata jama'a su kiyaye da su lokacin zafi:
1. A ke yawaita shan ruwa. Ruwan da bai yi sanyi kau ba ya fi lafiya ga jiki.
2. A kula da tsaftar jiki da tsaftace kananan yara marasa wayo
3. A cire ciyayi dake cikin gida da waje domin hana kwari kamar su macizai, tsaka, kulba, shashani, kunama da sauran kwari samun mazauni.
4. A guji kashe maciji, saboda a cikin macizai akwai masu matukar hadari da shu'umanci.
5. Za a iya amfani da magungunan kawar da macizai da kwari na zamani ko na gargajiya macizai shigowa gida.
DUBA WANNAN: Akwai sarakuna da ke hada baki da 'yan bindiga a Zamfara - Ministan tsaro
6. A kula sosai wajen barin tagogi da kofofi a bude domin samun kwararar iska, wasu kwari ko kananan dabbobi masu guba kan iya shiga daki ta kofa ko taga. Saka murfin kofa mai raga zai taimaka sosai.
7. Domin guje wa cin karo da macizai da wasu kwari ko kananan dabbobi masu guba, a tabbatar an duba rassan itatuwa da kuma tarin ganye ko surkukin dake karkashin itatuwa
8. Tsaftace muhalli da rufe kayan abinci zai taimaka wajen guje wa kamuwa da cutatuka daga guba ko gurbatacewar abinci.
9. A yi amfani gidan sauro domin gujewa kamuwa da Zazzabin cizon sauro.
10. A kiyaye cin wasu nau'ikan abinci kamar su wake, madara, kifi da sauran su idan dare ya yi dominkauce wa matsalar rudewa ko ciwon ciki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng